Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A watan jiya, Trump ya ce Amurka ta shirya kai hari a Nijeriya domin kawar da masu yi wa "Kiristoci kisan gilla."

Amurka ta ƙulla yarjejeniya da Nijeriya don mayar da hankali kan kyautata kiwon lafiyar Kiristoci

Amurka ta sanar da cewa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya don ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na Nijeriya, 'yan makonni bayan Shugaba Donald Trump ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.

A ƙarƙashin yarjejeniya ta shekaru biyar, Washington za ta bayar da kusan dala biliyan 2.1 don taimakawa wajen hana yaɗuwar HIV, tarin fuka, zazzaɓin cizon sauro da cutar polio, da kuma kare lafiyar mata masu juna biyu da yara, in ji wani mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka a ranar Asabar.

Nijeriya ta yi alƙawarin kashe ƙarin kusan dala biliyan 3 a cikin shekaru biyar masu zuwa, in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, yana mai ƙarawa da cewa yarjejeniyar ta ƙunshi "mayar da hankali kan tallafa wa cibiyoyin kiwon lafiya masu alaƙa da addinin Kiristanci."

A watan jiya, Trump ya ce Amurka ta shirya kai hari a Nijeriya domin kawar da mutanen da ya ce suna yi wa "Kiristoci kisan gilla."

Shugaban Amurka ya ce Kiristanci na fuskantar "barazana ta gushewa" daga Nijeriya da "ƙasashe da dama," yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta bari a ci gaba da tsangwamar Kiristoci ba.

Washington ta sanya Nijeriya a cikin jerin ƙasashe da ake "sanya wa idanu sosai" dangane da 'yancin addini kuma ta taƙaita bayar da biza ga 'yan Nijeriya.

An ƙulla wannan yarjejeniyar ce "bayan gwamnatin Nijeriya ta yi wasu gyare-gyare domin bayar da fifiko ga kare Kiristoci daga tashin hankali," in ji mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen.

Mahukuntan Nijeriya sun sha bayyana cewa ba a nuna tsangwama ga mabiya kowane addini.

Nijeriya ta daɗe tana fama da rikice-rikice na ƙabilanci da addini da kuma na ƙungiyoyin da ke iƙirarin jihadi, kuma rikicin ya halaka aƙalla mutane 40,000, ciki har da Kiristoci da Musulmai, tare da tilasta wa kusan mutane miliyan biyu yin gudun hijira, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

A farkon watan Disamba, Amurka ta sanya hannu kan yarjejeniyar tallafin kayan kiwon lafiya ta dala biliyan 2.5 da Kenya - wannan ita ce yarjejeniya ta biyu tun bayan da Trump ya soke hukumar USAID da ke tallafa wa ƙasashen duniya musamman kan harkokin lafiya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#