Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Abubuwan da ke cikin motocin da aka kama sun haɗa da safaya taya guda 31, rim ɗin mota guda 23, kekuna guda biyu, makullan mota guda 12, buhunan gawayi da sauran kayayyaki.
Sojojin Rundunar Operation Hadin Kai sun cafke motocin a-kori-kura guda biyu da ake zargin suna ɗauke da kayayyaki ga ’yan ta’addar ISWAP a Jihar Borno.
Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.
Sani ya ce an gudanar da aikin ne bayan samun sahihin bayanan sirri daga jama’a, inda aka sanar da hedikwatar rundunar game da motsin ‘yan ta’addan inda suke jigilar kayayyakin daga Dapchi a Jihar Yobe zuwa yankin Magumeri na Jihar Borno.
Bayan samun bayanan sirrin, nan take aka aika dakaru domin tare motocin ‘yan sandan a hanyar da aka gano a su bi.
A cewarsa, an ƙwato abubuwa da dama da suka haɗa da motocin farar-hula guda biyu, safaya taya guda 31, rim ɗin mota guda 23, kekuna guda biyu, makullan mota guda 12, altaneta ta mota guda uku, buhunan gari guda biyu.
Haka kuma sauran abubuwan sun haɗa da katifa guda ɗaya, buhunan gawayi guda biyar, doya guda 34, barguna guda biyu, ledojin garri guda biyu, tufafin manya da na yara iri-iri, na’urar power bank guda ɗaya, wayoyin hannu guda shida, da kuma wasu kuɗaɗe na nau’uka daban-daban.
Ya tabbatar wa jama’a cewa sojojin za su ci gaba da jajircewa wajen hana ’yan ta’adda ’yancin motsi, katse hanyoyin samar musu da kayayyaki, da kuma tabbatar da tsaro da lafiyar ’yan ƙasa masu bin doka a duk faɗin yankin Arewa maso Gabas.
Comments
No comments Yet
Comment