Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Yakin Isra'ila a Gaza ya jefa Falasdinawan Gaza 'sama da 400,000' cikin talauci

05:30 GMT — Yakin Isra'ila a Gaza ya jefa Falasdinawan Gaza 'sama da 400,000' cikin talauci

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda tattalin arzikin Falasdinu yake rushewa bayan Israila ta kwashe fiye da wata daya tana yi wa Gaza luguden wuta tare da yi wa daukacin yakin kawanya.

Tattalin arzikin Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gaza ya fadi da kashi hudu cikin dari lamarin da ya jefa fiye da mutum 400,000 cikin talauci — abin da ba a taba gani ba a yakin Syria da na Ukraine, da ma yake-yaken da aka yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa na yankin Gaza a baya.

Isra'ila ta lalata ko ta rusa akalla kashi 45 cikin dari na dukkan gidajen Gaza, a cewar wata kididdiga da Shirin Majalisar Dinkin Duniya na Ci-gaba UN Development Program da kuma na Tattali Arziki da Walwala a Yankin Asiya wato UN Economic and Social Commission for West Asia suka fitar.

#