Wannan shafin ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0850 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 240 tun bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta
Kungiyar Hamas ta ce mutum 240 aka kashe a Gaza da ke Falasdinu tun bayan da aka kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a ranar Juma'a.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an raunata karin mutum 650 a "daruruwan hare-hare ta sama da makaman atilare da bama-bamai daga sojojin ruwa a Zirin Gaza", in ji sanarwar,
Sanarwar ta ce sojojin na Isra'ila sun mayar da hankali wurin kai hare-hare a Khan Younis inda aka lalata gomman gidaje da mazauna cikin gidajen.