Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 80 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,500, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,036.
0000 GMT —Isra'ila ta kashe mutum 78 a hare-haren da ta kai Gaza a jajibirin Kirsimeti
Jami'an lafiya na Falasdinu sun ce wasu hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a jajibirin Kirsimeti sun yi sanadin mutuwar mutum akalla 78.
Isra'ila ta kaddamar da hare-haren ne da tsakar daren Litinin inda ta wayi garin yau tana luguden wuta musamman a yankin Al Bureij da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda ganau da kafafen watsa labarai na Falasdinu suka tabbatar.
An kashe akalla mutum 70 a hari ta sama da jiragen yakin Isra'ila suka kai yankin Maghazi da ke tsakiyar Gaza, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar Falasdinu Ashraf Al Qidra, yana mai cewa galibinsu mata ne da kananan yara.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana nazari kan abin da ya faru a Maghazi kuma tana so ta rage yawan fararen-hular da ke cutuwa. Kungiyar Hamas ta musanta zargin da Isra'ila ke yi mata cewa tana buya a wuraren da ke da dandazon jama'a inda take yin amfani da mutanen a matsayin garkuwa.
Kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta wallafa bidiyoyin mutanen da suka jiakkata a yayin da ake tafiya da su asibiti. Ta ce jiragen yakin Isra'ila sun yi ta luguden wuta a manyan hanyoyin da ke tsakiyar Gaza, inda suka hana motocin daukar marasa lafiya wucewa.
