Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 95 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 23,210tare da jikkata 59,167 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira.
1625 GMT — An kashe sojojin Isra'ila tara a kwana guda
Isra’ila ta sanar da cewa an kashe mata sojoji tara a cikin kwana guda a yakin da take yi a Gaza.
Tun da farko Isra’ilar ta sanar da cewa an kashe mata sojoji hudu a yakin da take yi da Falasdinawa a kudanci da tsakiyar Gaza, sannan aka raunata shida.
Sai dai daga baya ta kara fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da kashe wasu karin sojojin nata biyar.
Zuwa yanzu an kashe sojojin Isra’ila sama da 520 tun daga soma yakin a ranar 7 ga watan Oktoba.