Dollar

40,2599

0.13 %

Euro

46,8125

0.26 %

Gram Gold

4.319,6800

0.52 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe shekara guda tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 41,870. Kazalika, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon tun Oktoban 2023 inda ta kashe fiye da mutum 2,000, ta raba fiye da mutum miliyan 1.2 da muhallansu.

Kai-tsaye: Amurka ta gargaɗi Isra'ila kada ta kai hari a filin jiagen saman Beirut

Talata, 8 ga watan Oktoba, 2024

2052 GMT — Amurka ta gargaɗi Isra'ila kada ta kai hari a filin jiragen saman Beirut ko kuma hanyoyin da ake bi domin isa filin, a yayin da sojojin Isra'ila suka kai manyan hare-hare a yankunan da ke bayan babban birnin na Lebanon.

"Muna gani yana da matuƙar muhimmanci filin jiragen saman ya kasance a buɗe, yana kuma da muhimmanci hanyoyin da ake isa filin su zama suna aiki, ta yadda Amurkawa da ke son barin yankin za su samu damar bari, kuma su ma 'yan sauran ƙasashe za su samu damar barin yankin," in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller a hira da manema labarai.

2050 GMT — Hezbollah ta kai hari a cibiyar tattara bayanan sirri da ke Tel Aviv

Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta kai hari da wani makami mai linzami kan cibiyar tattara bayanan sirri da ke gefen birnin Tel Aviv.

2038 GMT — Isra'ila ta ce an harba mata makamai biyar daga Lebanon

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce an harba mata aƙalla makamai biyar daga Lebanon, ko da yake ta kakkaɓo wasu daga cikinsu.

"Bayan jiniya ta yi ƙara a wasu yankuna da ke tsakiyar Isra'ila, an gano makamai biyar da aka harbo daga Lebanon zuwa cikin Isra'ila," a cewar wata sanarwa da rundunar sojojin Isra'ila ta fitar.

"Rundunar sojojin sama ta IAF ta kakkaɓo wasu daga cikinsu, yayin da sauran suka sauka a fili (inda babu mutane)."

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#