Dollar

39,1011

0.04 %

Euro

44,4609

0.52 %

Gram Gold

4.202,2600

1.92 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Sama da mutane 36,000 aka kashe a yankuna 14 da ake yake-yake a 2024 a duniya, in ji Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis.

Aƙalla mutum 36,000 aka kashe a yaƙe-yaƙe a duniya a 2024: MDD

Shugaban ayyukan jin kai na MDD ya bayyana damuwa a ranar Alhamis sakamakon illatuwar fararen hula a rikice-rikicen duniya, inda ya kuma bayyana cewa sama da fararen hula 36,000 ne aka kashe a yankuna 14 da ake rikici a 2024.

“Akwai yiwuwar adadin ya fi haka,” Tom Fletcher ya fada wa Kwamitin Tsaro a yayin gudanar da taro kan kare fararen hula a yankunan da ake da rikici.

Ya yi gargadi kan hatsarin da ke tunkarar duniya. “Muna shaida ake keta dokokin kasa da kas aba a kare fararen hula tare da girmama dokokin’ ayyukan jin kai.”Ya kaa fafa.

Fletcher ya kara da cewa addin wadanda aka raba matsugunansu ya kai saa da miliyan 122, inda mafi yawa aka raba da su da matsugunansu a cikin kasashensu.

Yunwar da yake-yake suka janyo ta yi tsamari

Ya kara da cewa an samu rahotannin batan mutane, zaluntar jama’a, mummunar mu’amala da sauran musgunawa.

“Cin zarafin mata ya yawaita,” in ji Fletcher. “MDD ta tabbatar da cin zarafin mata sau 4,500 a shekarar da ta gabata, inda kashi 93 manyan mata da yara mata ne.”

Ya kara da cewa yunwar da yake-yake suka janyo ta kai wani mummunan yanayi, kuma “2024 shekarar da aka fi samun mutuwar ma’aikatan jin kai,” inda aka kashe sama da ma’aikatan agaji 360. ciki har da 200 a Gaza da 54 a Sudan.

Da yake kira ga Kwamitin da dauki matakan shari’a don kariya da aiki da gaskiya, ya ce “Wasu Kasashen duniya na zabar dokokin da za su yi aiki da su, ya ta’alaka da su waye ake magana a kai. Duk wannan na raunata manufar dokokin yaki: a rage shan wahalar dan adam a rikici da makamai.”

Sama da mata manya da yara miliyan 612 na rayuwa a yankunan da ake rikici

Daraktar Hukumar Kula da Mata ta MDD, Sima Bahous ta yi gargadin cewa “sama da mata manya da yara miliyan 612 na rayuwa a yankunan da ake rikici,” inda ta kira hakan da “Kira gare mu baki daya da mu dauki mataki”.

“A Gaza, an kashe mata manya da yara sama da 28,000 tun Oktoban 2023, kamar duk awa daya an kashe mace guda kenan,” in ji ta. “Wadannan ba dalilan afuwar yaki da aka saba gani ba ne. Sun afkuwa ne saboda rikicin da ake ta maimaitawawa.”

Ta jaddada cewa akwai bukatar gaggawa don yin adalci. “In banda a ‘yan wasu wurare, ba a hukunta masu hannu a rikicin. An diana saka takunkumai ga kasashe,” in ji Bahous.

Ta yi gargadin cewa katse tallafin kudade na barazana ga farfadowar mata.

‘Wata sabuwa, sabbin rikice-rikice’

Shugabar Kungiyar Bayar da Agaji ta kasa da kasa ta Red Crescent Mirjana Spoljric ta yi kira ga a bayar da kariya ga dokar jin kai ta kasa da kasa: “Kasar na iaya zama marar fuskantar yaki a yau. Danginka na iya zama a sahun gaba, sai abubuwa su sauya, yaki ya barke, to idan ba ku kare dokokin kasa da kasa ba a yau, kenan kuna aminta da duniyar da za a yi ta yake-yake munana tare da watsi da mutuntaka.”

Spoljric ta tunatar da cewa har yanzu tirsasawa mutane su bar matsugunansu a yankunan da aka mamaya ba ya bisa ka’ida.

Janti Soeripto, shugabar Save the Children a Amurka, ta bayyana irin raunin da yara ke ciki a yankunan da ake yaki: “Yara ba matasa ba ne.”

“Ba za a taba samun zaman lafiya ba idan babu adalci kuma idan babu gaskiya babu kariya,” in ji ta. Ta kuma bukaci Kwamitin da ya gudanar da bincike na gaskiya tare da taimaka w ayaran da suka kubuta.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#