Sport
Dollar
38,9244
0.13 %Euro
44,1570
0.11 %Gram Gold
4.138,2500
-0.11 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban Amurka Donald Trump da jakadan Isra'ila a Amurka sun yi Allah wadai da wannan lamarin inda suka kira shi da ƙin jinin Yahudawa
An kashe ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ila biyu a wajen gidan adana kayan tarihi na Yahudawa da ke birnin Washington a ranar Laraba da dare, kamar yadda hukumomin Amurka suka tabbatar.
Mutanen da aka kashe waɗanda mace da namiji ne, an harbe su da bindiga a kusa da kusa a daidai lokacin da suke ficewa daga gidan adana kayan tarihin bayan wani biki da aka yi a gidan wanda ke zagaye da manyan ma’aikatun gwamnatin Amurka, ciki har da ofishin tsaro na FBI.
“An kashe ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ila biyu cikin rashin hankali a daren yau a kusa da gidan adana kayan tarihin Yahudawa a birnin Washington DC,” kamar yadda sakatariyar hukumar tsaro ta US Homeland Security, Kristi Noem ta bayyana, inda ta ce za a bi wa waɗanda aka kashe haƙƙinsu.
Nan take ‘yan sanda suka mayar da martani inda suka rufe tituna da dama da ke kusa da wurin da kuma rufe jami’ar Georgetown da ke Capitol.
Shugaban Amurka Donald Trump da kuma jakadan Isra’ila a Amurka duk sun yi Allah wadai da wannan harin inda suka kira harin da ƙin jinin Yahudawa.
A yayin wani taron manema labarai, jakadan na Isra’ila a Amurka Yechiel Leiter ya ce mutanen da aka kashe masoya biyu ne Yahudawa waɗanda ke shirin aure.
Comments
No comments Yet
Comment