Dollar

39,1461

-0.03 %

Euro

44,8210

0.41 %

Gram Gold

4.233,7000

0.28 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Rasha ta tabbatar da karɓar daftarin Ukraine kan sulhun gabanin zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu a Fadar Ciragan a Istanbul ranar Litinin.

Duniya na jiran tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine a Istanbul yayin da yaki ke kara kamari

Dukkan idanu sun karkata zuwa Istanbul yayin da ake jiran tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine da aka shirya yi a ranar Litinin, inda tuni wakilan ɓangarorin biyu suka isa birnin.

Ana sa ran za a fara zagaye na biyu na tattaunawar tsakanin ɓangarorin biyu zai gudana ne da misalin a 1000 agogon GMT ranar Litinin a Fadar Ciragan mai tarihi da ke Istanbul.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai jagoranci taron, wanda zai haɗa manyan jami'ai daga ƙasashen uku. Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Kasa (MIT) na Turkiyya, Ibrahim Kalin, shi ma ana sa ran zai halarta.

Bayan ɓarkewar yaƙin a watan Fabrairu 2022, Turkiyya ta kawo Rasha da Ukraine a tebur guda a Antalya da Istanbul.

A watan Mayu na wannan shekarar, Turkiyya ta sake samun nasarar karaɓr baƙuncin ɓangarorin biyu don tattaunawa ta farko cikin fiye da shekaru uku na rikici. Tattaunawar ta gudana a ranar 16 ga Mayu a Fadar Dolmabahce da ke Istanbul.

Ɓangarorin biyu sun amince da musayar fursunoni 1,000 kowanne a tattaunawar ranar 16 ga Mayu, tare da gabatar da ra'ayoyinsu kan yiwuwar tsagaita wuta da ci gaba da tattaunawa. Sun sanar da cewa musayar fursunonin ta kammala a ranar 25 ga Mayu.

Da dama daga cikin masu ruwa da tsaki na Ƙasa da Ƙasa sun bayyana jin ɗaɗinsu da fara wannan tsari a Istanbul, kuma tattaunawar da Turkiyya ta karɓi baƙunci ta samu karɓuwa sosai a kafafen yaɗa labarai na duniya.

Turkiyya na ci gaba da ƙoƙarin shiga tsakani

Turkiyya ta ci gaba da aiki don samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, inda Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya ziyarci Moscow daga 26-27 ga Mayu da kuma Kiev daga 29-30 ga Mayu.

A Moscow, Fidan ya gana da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, tare da gudanar da tarurruka da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Lavrov, da wasu manyan jami'ai.

Lavrov ya bayyana cewa suna martaba ƙoƙarin Turkiyya na sake samar da damar tattaunawa kai tsaye tsakanin Rasha da Ukraine.

A ranar 28 ga Mayu, Lavrov ya sanar da cewa sun bai wa Ukraine shawarar gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa a Istanbul ranar 2 ga Yuni.

Shugaban tawagar Rasha, Vladimir Medinsky, ya tabbatar da cewa sun karɓi takardar shawarwarin Ukraine kan warware rikicin cikin lumana.

Ministan Tsaron Ukraine zai jagoranci tawagar a Istanbul

Bayan ziyararsa zuwa Rasha, Fidan ya kai ziyara aiki zuwa birnin Kiev na Ukraine.

Shugaban Ukraine ya bayyana cewa, duk da rashin samun wani tayin tsagaita wuta daga Rasha, gwamnatinsa na fatan samun ci-gaba a Istanbul.

Tashin hankali ya kara ƙamari kafin tattaunawar

A yayin da ɓangarorin ke shirin zama a teburin tattaunawa a Istanbul, an samu rahotannin hare-hare masu tsanani a ƙarshen mako.

Hukumar Tsaron Ukraine (SBU) ta ce dakarunta sun kai hari mai girma kan Rasha, inda suka lalata jiragen yaki sama da 40 a hare-haren da aka kai ta amfani da jiragen sama marasa matuka.

Ma’aikatar Tsaron Rasha ta bayyana hare-haren a matsayin “hare-haren ta’addanci” da gwamnatin Kiev ta dauki nauyi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#