Sport
Dollar
40,5953
0.02 %Euro
46,5953
0.56 %Gram Gold
4.299,6100
0.6 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hukumar sa ido kan girgizar kasa ta Rasha ta ce girgizar ƙasar wadda ta afku a ranar Laraba ta kasance mafi girma da aka taɓa fuskanta tun shekarar 1952 a yankin Kamchatka na kasar, inda ta yi gargadi kan abin da ka iya biyo baya.
Daya daga cikin girgizar kasa mafi girma da aka taba fuskanta a Rasha ta afku ne a yankin Gabas mai nisa wanda ke da karancin jama'a a kasar da sanyin safiyar ranar Laraba.
Lamarin ya haddasa ambaliyar tsunami da zurfinta ya kai mita hudu (kafa 12) a faɗin Tekun Pacific har ya janyo ƙaurar jama’a daga yankin Hawaii zuwa Japan.
Girgizar ƙasar mai karfin maki 8.8 ta afku ne da misalin karfe 8:24 na safiyar ranar Laraba agogon ƙasar, a kusa da yankin Petropavlovsk da ke gabar tekun Kamchatka na Rasha, kuma ta kasance daya daga cikin girgizar kasa mafi girma a cikin guda 10 da aka taba fuskanta a kasar, a cewar Cibiyar Binciken Kasa ta Amurka.
Hukumomin Rasha sun ce ambaliyar tsunamin ta afku tare da mamaye garin Severo-Kurilsk mai tashar jiragen ruwa, yayin da kafofin yada labaran kasar suka ce daya daga cikin ambaliyar da toroƙonta ya kai mita uku zuwa hudu ta afku ne a gundumar Elizovsky na Kamchatka.
Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta na Rasha ya nuna yadda gine-gine a garin suka yi ta nutsewa cikin ruwan teku. Hukumomi sun ce an kwashe mutane 2,000 a yankin.
Mutane da dama ne suka jikkata a kasar Rasha sakamakon ambaliyar, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito, amma babu wani daga cikinsu da ya yi tsanani.
"Bangwaye na ta girgiza." kamar yadda wata mazauniyar Elizovsky ta shaida wa kafar yada labaran Zvezda.
"Mun yi koƙarin ɗaukar akwati, akwai wanda ke dauke da ruwa da kuma tufafinmu a kusa da kofa, da sauri muka ɗauka muka fita da gudu... Abin ya ban tsoro," in ji ta.
Jami'ai daga kasashen da ke a gabar Tekun Pacific a Arewa da Kudancin Amurka - wadanda suka hada da Amurka, Mexico da Ecuador - sun fitar da sanarwar gargadi don guje wa rairayin bakin teku na wuraren da lamarin ya shafa.
A Japan, an yi ta kwashe mutane da mota da ƙafa zuwa wurare da ke kan tudu - ciki har da Hokkaido, inda aka samu ambaliyar farko da ya kai santimita 30.
Ba a samu rahoton waɗanda suka ji rauni ko wata ɓarna ba a Japan ba har zuwa faɗuwar rana (0300 GMT).
A Hawaii, Magajin Garin Honolulu Rick Blangiardi ya buƙaci mazauna garin da dubban baƙi su samu tsaro a saman benayen gine-gine ko kuma a ƙasa da ke da tudu.
"Kamar yadda muka gani a baya, bai kamata mutane, ina sake maimaitawa, su tsaya a bakin teku ko kuma su yi kasada da rayukansu don kawai su ga yadda ambaliyar tsunami take kasancewa ba," in ji gwamna Josh Green.
‘‘Ba ambaliyar da aka saba gani ba ce. Tabbas mutum zai iya mutuwa idan har tsunami ta bige shi,’’ in ji Green.
Gargadi a dukkan yankunan Pacific
Karfin girgizar ƙasar ya kusan yin daidai da girman nau'in 9.0 da ya afku a bara wanda ya haifar da barna da ambaliyar tsunami a yankin Pacific, a cewar USGS.
Akalla girgizar kasa guda shida yankin ya taba fuskanta, cikin har wadda ta ta kai girman maki 6.9 da kuma wata da ta kai maki 6.3.
Cibiyar Gargadi kan Tsunami ta Amurka ta ce igiyar ruwa da ta zarce mita uku sama da magudanar ruwa na iya afkuwa a wasu gabar tekun Ecuador da tsibiran Hawai da ke arewa maso yammacin kasar da kuma Rasha.
Akwai yiwuwar kasancewar igiyar ruwa mai tsawon mita daya zuwa uku a wasu gabar teku na Chile,da Costa Rica, da na Faransa Polynesia, da Guam, da Hawaii, da Japan da kuma sauran tsibirai a yankunan Pacific, a cewar sanarwar gargadin.
Karfin guguwar igiyar ruwan ya kai mita daya a wasu wurare, ciki har da Australia, Colombia, Mexico, New Zealand, Tonga da Taiwan.
Ta bayyana yuwuwar yanayi a matsayin "masu haɗari".
Hotunan talabijin sun nuna wasu manyan kifayen da ambaliyar ta watso su zuwa bakin teku.
An kwashe ma'aikatan tashar Nukiliya ta Fukushima da ke arewa maso gabashin Japan - wadda wata babbar girgizar kasa da igiyar ruwa ta tsunami ta lalata a shekarar 2011 , a cewar sanarwar cibiyar.
Kazalika ita ma Taiwan ta sanya agogon ankararwa kan tsunami, kana Hukumar Kula da Yanayi ta kasar ta yi gargadin cewa igiyar ruwan Tsunami na iya isa gabar tekun Taiwan da misalin karfe 1.18 na rana. (0518 GMT).
A bangare guda kuma kasar Philippines ta gargadi mazauna yankunan da ke kallon gabar Tekun Pacific kan wani" igiyar ambaliyar tsunami da ba ta gaza mita ɗaya ba" biyo bayan girgizar kasa mai karfin gaske da ta afku.

Bayan girgizar kasa
An aika da sanarwar gargaɗi kan tsunami ta wayoyin hannu a California, a cewar manema labarai na AFP na cikin gida.
"KU ZAMA JARUMAI KUMA CIKIN SHIRI!" kamar yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na soshiyal midiya.
Ƙararrawar Tsunami ta barke a kusa da fitaccen bakin Tekun Waikiki na Hawai inda wani mai daukar hoto na AFP ya ɗauki cunkoson ababen hawa yayin da 'yan Hawaii suka tsere zuwa wurare masu tsaro da ke da tudu.
Cibiyoyin Gargadin Tsunami na Amurka sun fitar da sanarwar gargaɗin Tsunami -- gargadɗi mafi girma - ga ɗaukacin al’ummar jihar Hawaii ta Amurka, kana ana sa ran za a guguwar igiyar farko zai afku da misalin ƙarfe 7:17 na yamma agogon ƙasar (0517 GMT).
"An kuma shawarci mutane da su nesanta kansu daga bakin tekun," a cewar sanarwar gargaɗin Cibiyar Nazarin Yanayin Kasa .
An umurci jiragen ruwa da su nufi wurare da ke da tsaro gabanin isowar igiyoyin ruwa das aka yi hasashen zai kai mita biyu.
Comments
No comments Yet
Comment