Sport
Dollar
40,5928
0 %Euro
46,9965
0.15 %Gram Gold
4.345,0000
0.11 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Gwamnatin China ta fara bayar da tallafi ga iyaye don sauƙaƙa musu wahalhalun kula da 'yaya, da nufin ƙara yawan haihuwa a ƙasar.
A ranar Litinin, China ta ƙaddamar da tallafin shekara-shekara na kula da yara ƙanana da ya kai yuan 3,600 ($502) har yara su kai shekaru uku, domin bunƙasa yawan haihuwa da ke raguwa a ƙasar.
Hukumomi sun nuna damuwa kan yadda matasa da dama ke ƙin haihuwa, yayin da adadin tsofaffi ke karuwa.
Tsadar kula da yara da ilimi, da rashin tabbas a fannin ayyukan yi, da koma bayan tattalin arziki na daga dalilan da suke hana matasa a China da yawa yin aure da tara iyali.
Tallafin zai fara aiki daga farkon wannan shekarar, tare da tallafi na wani bangare ga yara 'yan kasa da shekaru uku da aka haifa kafin 2025, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na China Xinhua, wanda ya ce wannan manufa za ta amfani iyalai sama da miliyan 20 da ke da jarirai da ƙananan yara.
Wannan shirin, a cewar Hukumar Kiwon Lafiya ta Kasa, yana da matukar muhimmanci ga rayuwar al'umma, kuma bayar da tallafin kudi kai-tsaye zai taimaka wajen rage kuɗin haihuwa da kula da yara ga iyalai.
A karshen shekarar 2024, kasar Sin ta samu mutane miliyan 310 da suka kai shekaru 60 da haihuwa ko fiye. Jimillar yawan al'ummar kasar Sin ya kai kimanin biliyan 1.41, bisa ga bayanan da Worldometer ya tsara daga sabbin bayanan Majalisar Dinkin Duniya.
Raguwar Yawan Jama'a
Yawan al'ummar kasar Sin ya ragu a shekara ta uku a jere a shekarar 2024, inda masana suka yi gargadin cewa matsalar na iya ƙara tsananta, bayan shekaru da dama na rage haihuwa, sakamakon manufar haihuwa daya da aka aiwatar daga 1980 zuwa 2015, tare da saurin bunƙasar birane.
A cikin shekaru biyu da suka gabata, jihohi a fainɗ kasar sun fara bayar da tallafin kula da yara ƙanana da ke da bambanci sosai, daga yuan 1,000 ($139) ga kowanne yaro zuwa yuan 100,000 ($13,931), ciki har da tallafin gidaje.
Gwamnatin ƙasa za ta ɗauki nauyin wannan sabon shirin a ƙasa baki ɗaya, maimakon hukumomin jihohi, a cewar Xinhua.
Kula da yara a ƙasar China na ɗaya daga cikin mafi tsada a duniya idan aka kwatanta da matakin samun kuɗin shiga, a cewar wani bincike da aka yi a China.
Hukumomi sun ƙaddamar da jerin matakan da za su “bunƙasa haihuwa” a shekarar 2024 domin tunkarar ƙalubalen da ake sa ran zai taso a cikin shekaru goma masu zuwa, lokacin da mutane kimanin miliyan 300 za su yi ritaya, wanda ya yi daidai da kusan yawan al'ummar Amurka baki ɗaya.
Comments
No comments Yet
Comment