Dollar

40,5864

0.02 %

Euro

46,3592

-1.14 %

Gram Gold

4.272,1700

-1.57 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

The virus spreading beyond Indian Ocean into Africa, South Asia, and Europe, says WHO's team lead on arboviruses.

Mece ce cutar chikungunya, kuma me ya sa WHO ta damu a kanta?

A ranar Talata ne Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi gargadin cewa duniya ka iya sake fuskantar annobar cutar chikungunya da aka yi fama da ita a shakarar 2005 idan har ba a ɗauki matakin da ya dace na daƙile yaɗuwarta ba.

"Chikungunya cuta ce da ba a santa ba sosai, amma tuni yana yaɗuwa a ƙasashe 119, tana saka mutum biliyan 5.6 a cikin haɗari,” kamar yadda Diana Rojas Alvarez, jagoran tawagar WHO mau yaƙi da cututtukan ƙwayoyin virus da irin waɗanda sauro ke janyowa, ya faɗa a wani taron MDD.

Cutar wacce sauro ke jawowa tana haddasa zazzai da ƙuraje da ciwon gaɓoɓi mai tsanani da za a shafe makonni ana fama da su, ko kuma ta jawo nakasa ga kashi 40 cikin 100 na waɗanda suka kamu.

Tun farkon shekarar 2025 ne aka samu ɓrkewar cutar a wasu tsibiran Tekun Indiya da suka haɗa da La Reunion da Mayotte da kuma Mauritius, inda aka yi ƙiyasin cewa kashi ɗaya bisa uku na al’ummar La Reunion sun kamu, in ji Rojas.

A cewarta, a yanzu cutar na ƙara yaɗuwa zuwa cikin Madagascar da Somalia da Kenya, yayin da ake cigaba da samun ɓarkewarta a Kudancin Asiya sakamakon ɓarkwarta annobarta da aka samu a Indiya a 2024.

Limiting infections Rage tasirin cutar

Sri Lanka da Bangladesh sun ce ana samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar, sannan an gani ɓullarta a Turai, ciki har da Faransa da Italiya.

“Yanayin yaɗuwarta yana nuna irin abin da muka gani a shekarun 2004 da 2005,” kamar yadda Rojas ta yi garaɗi. “Dole ne mu yi wani abu yanzu don hana tarihi maimaita kansa.

Ta kuma jaddada buƙatar ƙasashen da ake da sauro nau’in Aedes wato mai fari-fari a jikinsa da su ɗauki matakan daƙile yaɗuwar su.

SDuk da cewa a yanzu ana samun raguwar masu kamuwa da cutar a Tekun Indiya saboda gabatowar lokacin hunturu, ta jaddada cewa gano ta da wuri da ɗaukar matakin gaggawa su ne muhimman hanyoyin rage tasirinta a kan lafiya da tattalin arziki.

WHO tana taimakon ƙasashe ta hanyar kai musu ƙwararru da gogaggun ma’aikatan lafiya da goyon bayan ɗuakar matakan kariya, in ji ta.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#