Dollar

40,5936

0.02 %

Euro

46,5897

0.55 %

Gram Gold

4.303,5300

0.69 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Yanayin da ake ganin yaran Gaza na ciki a ‘yan kwanakin nan ya yi matuƙar kaɗa duniya.

Fiye da Ƙasashen Yamma 14 na kira da a amince da samar da ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta

Faransa da wasu Ƙasashen Yammacin Duniya 14 sun yi kira ga sauran ƙasashe a faɗin duniya da su amince da samar da ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta, kamar yadda wani babban jami’in diflomasiyya na Faransan ya faɗa a ranar Laraba.

“A birnin New York, tare da wasu ƙasashen 14, Faransa tana miƙa roƙo na haɗin-gwiwa: muna miƙa buƙatarmu ta a amince da kafa ƙsar Falasɗinu mai cin gashin kanta, tare da gayyatar waɗanda har yanzu ba su bi wannan sahu ba,” a cewar Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, a wani saƙo da ya wallafa a shafin X, bayan taron da aka yi don farfaɗo da batun samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu ga Isra’ilawa da Falasɗinawa.

A hannu guda kuma, Birtaniya ta yi watsi da sukar da Isra’ila da Amurka suka yi mata na cewa tana goyon bayan Hamas ne ta hanyar fitar da shirye-shiryen amincewa da kasa ƙasar Falasɗinu idan har Isra’ila ba ta ɗauki matakin inganta yanayin da ake ciki ba a Gaza da kuma samar da zaman lafiya.

“Wannan batu ne da ya shafi Falasɗinawa. Batu ne da ya shafi yaran da muke gani a Gaza waɗanda yunwa ke kashe su, kamar yadda Ministan Sufuri na Birtaniya, Heidi Alexander ya shaida wa gidan rediyon LBC a ranar Laraba.

“Dole ne mu matsa wa gwamnatin Isra’ila lamba ta ɗage takunkuman da ta sanya don a samu damar isar da kayan agaji cikin Gaza.”

Yanayin da ake ganin yaran Gaza na ciki a ‘yan kwanakin nan ya yi matuƙar kaɗa duniya.

Ƙungiyoyin da ke sa ido kan yunwa na gargaɗi cewa mafi munin yanayi na rashin abinci da yunwa zai cigaba da faruwa, kuma ana buƙatar ɗaukar matakai nan da nan don kare samun ƙrin mace-mace.

A wani jawabi da ya gabatar a talabijin ranar Talata, Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce a yanzu lokaci ya yi, inda ya fayyace wahalhalun da ake sha a Gaza yana mai cewa fatan samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu a matsayin mafita ga zaman lafiya na cikin barazana.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#