Dollar

39,0323

0.28 %

Euro

44,0422

-0.02 %

Gram Gold

4.140,0000

0.41 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Mataimakin shugaban hukumar kwana-kwana ya ce cewa hatsarin jirgin, wanda ƙarami na masu amfanin kai ya yi kama da abubuwan da aka saba gani a fim.

Hatsarin jirgin sama ya kashe mutane da dama a California

Wani karamin jirgin sama ya fadi a wata unguwa a San Diego, jihar California a Amurka, inda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Sashen kashe gobara na San Diego ya bayyana a ranar Alhamis cewa jirgin mai zaman kansa ya fadi a wani gida na sojoji, inda ya lalata gidaje kusan 15, ya kuma haddasa gobara a gidaje da motoci da dama.

“Na duba lamarin da kaina a kan titin,abin ya yi kama dawanda muka saba gani a fim,” in ji mataimakin shugaban kashe gobara, Dan Eddy.

Forrest Gallagher, wanda ke zaune a yankin, ya shaida wa NBC News cewa ya ji “ƙara mai ƙarfi” wanda ya tashe shi daga barci.

“Na fita waje tare da maƙwabtana a kan titi kuma na ji wani wari mai ban mamaki, kamar wari na roba ko filastik da ke ƙonewa,” in ji Gallagher. “Na fita don bincike, sannan na ga wata mota tana ci da wuta.”

Eddy ya shaida wa manema labarai cewa mutane sun mutu, duk da cewa ba shi da cikakken adadi.

Ya ce jirgin na iya daukar mutane takwas zuwa goma, ciki har da matukin jirgin, amma hukumomi ba su san adadin mutanen da ke cikin jirgin lokacin da ya fadi ba.

Sai dai Eddy ya tabbatar cewa duk wadanda suka mutu suna cikin jirgin, kuma babu wanda ya mutu daga cikin mazauna unguwar.

“Muna da tabbacin cewa akwai wadanda suka mutu da yawa, amma za mu dauki lokaci mu tabbatar da abin da ya faru,” in ji Eddy.

Hukumar kashe gobara ta ce an kwashe mazauna unguwanni da dama a yankin saboda malalar man jirgin da hatsarin ya haddasa.

“Man jirgin sama ya malala a ko ina,” in ji Eddy ga manema labarai. “Muna da masu kula da sinadarai a wurin yanzu, kuma mun nemi karin kayan aiki don magance wannan matsalar.”

Shugaban ‘yan sandan San Diego, Scott Wahl, ya bayyana wurin hatsarin ga manema labarai, yana cewa akwai “man jirgin sama da ke gudana a kan titi, kuma komai yana ci da wuta lokaci guda.”

“Abin ya kasance mai ban tsoro sosai a gani,” in ji Wahl.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#