EU ta kuma ware dala miliyan 74 domin agajin jinƙai a ƙasar.

Gidauniyar Turkiyya Ta Raba Tallafin Ramadan Ga Iyalan Somaliya 8,250

Wata ƙungiyar agaji ta Turkiyya, Gidauniyar Turkiyya Diyanet (TDV), ta kai tallafin abinci ga iyalai 8,250 a yankunan da fari ya shafa a Somaliya a watan Ramadan. An rarraba kayan abincin a jihohi bakwai da yankuna 13, tare da mayar da hankali kan iyalan da ke fama da matsanancin hali sakamakon dogon fari.

Tawagogin gidauniyar da masu sa kai sun gudanar da rabon tallafin a wurare daban-daban, ciki har da sansanonin da ke Mogadishu, musamman a sansanin Hindere da ke gundumar Daynile da kuma sansanin Bilhayr a yankin Garapaley. Jami’ai sun ce tallafin na da muhimmanci yayin da fari da matsalar abinci ke ƙara tsananta.

A gefe guda, Tarayyar Turai (EU) ta sanar da bayar da dala miliyan 74 a matsayin tallafin jinƙai don tallafa wa al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a Somaliya. Tallafin zai mayar da hankali kan ayyukan ceton rai da suka haɗa da kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, tallafin kuɗi na gaggawa, ruwa da tsaftar muhalli, kariya da ilimin gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa kimanin mutane miliyan 6.5 na fuskantar tsananin yunwa a Somaliya, yayin da yara miliyan 1.85 ‘yan ƙasa da shekara biyar ke cikin haɗarin kamuwa da matsanancin rashin abinci mai gina jiki. EU ta ce za ta bayar da tallafin ta hanyar abokan hulɗa na jinƙai da ke aiki a ƙasar domin tabbatar da cewa taimakon ya isa ga masu buƙata.

Tushen labari: TRT Hausa

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#