Harin jirage marasa matuƙa ya lalata gine-gine a North Kordofan

Mayaƙan RSF sun kai hari a Jami'ar Kordofan

Jami’ar Jami’ar Kordofan ta ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai hari da jirage marasa matuƙa a reshenta da ke El-Obeid, inda suka lalata gine-gine da ababen more rayuwa da dama a ranar Litinin.

Sanarwar ofishin watsa labaran jami’ar ta ce an kai harin ne a gine-ginen da ke tsakiyar reshen jami’ar a El-Obeid, babban birnin jihar North Kordofan, lamarin da ya janyo lalacewa mai yawa. Ba a bayyana adadin mace-mace ba nan take.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Emergency Lawyers Association ta yi tir da harin, tana ɗora alhakinsa kan RSF, tare da cewa yana daga cikin jerin hare-haren da ake kai wa wuraren fararen-hula.

Ƙungiyar ta bayyana cewa kai hari kan makarantu da jami’o’i keta dokokin ƙasa da ƙasa ne, kuma yana barazana ga ‘yancin neman ilimi da makomar ɗalibai.

Yaƙin basasa ya ɓarke a Sudan tsakanin sojojin gwamnati da RSF tun watan Afrilun 2023, inda dubban mutane suka mutu, miliyoyi kuma suka rasa muhallansu, abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin jinƙai a duniya.

Tushen labari: TRT Hausa

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#