An kama mutane 33 tare da ƙwace makamai da miyagun ƙwayoyi

Dakarun Nijar Sun Kashe ’Yan Ta’adda 17 Cikin Mako Daya

Dakarun tsaron Nijar sun kashe ’yan ta’adda 17 tsakanin 16 zuwa 22 ga Fabrairu 2026, kamar yadda rahoto daga cibiyar haɗa kan ayyukan jami’an tsaro (CICO) ya bayyana.

Rahoton ya ce ayyukan sun kuma kai ga kama mutane 33 da ake zargi da aikata laifuka ko taimaka wa masu laifi da ake nema ruwa a jallo, inda aka miƙa su ga hukumomin da suka dace.

Haka kuma jami’an tsaron sun ƙwace nakiya 1,098, kilogram 48 na tabar wiwi, lita 23,250 na man fetur da aka samu ta haramtacciyar hanya, tare da daruruwan miyagun ƙwayoyi.

A cikin watan, an samu rahoton abubuwan fashewa sau uku, inda ƙwararrun jami’ai suka warware biyu daga cikinsu, yayin da na ukun ya fashe ba tare da jawo asarar rai ba.

Tushen labari: ANP

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#