Dollar

41,8410

0.03 %

Euro

48,7015

0.15 %

Gram Gold

5.615,6900

0.83 %

Quarter Gold

9.360,7700

0 %

Silver

69,9600

1.07 %

Wasan da Nijeriya za ta buga da Lesotho a maraicen Juma'ar nan zai zama mai haɗari ga damar Nijeriya ta cancantar buga kofin duniya na FIFA 2026.

Gasar Kofin Duniya ta 2026: Nijeriya za ta buga wasa biyu na ko-a-mutu-ko-a-yi-rai

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles na shirin neman kai bantenta a wasannin neman cancantar buga gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026. Wasanni biyu ne kacal suka rage a zagayen.

A maraicen yau ne Nijeriya ke fafatawa da Lesotho, kafin da karawarsu da Benin ranar 14 ga Oktoba, a zagayen wasa na 10 kuma na ƙarshe a nahiyar Afirka.

A halin yanzu, Nijeriya na mataki na uku a teburin Rukunin C, inda take da maki 11 daga wasanni takwas. Benin da Afirka ta Kudu ne a saman teburin da maki 14 kowannensu.

Sabon tsarin gasar Kofin Duniya ya ƙunshi ƙasashe 48, inda Afirka take da gurabe 9 na ƙasashen da za su samu tikiti kai-tsaye, da kuma ƙarin ƙasashe huɗu ga waɗanda suka fi maki cikin na biyu a rukunoni tara.

Fatan Afrika ta Kudu ta gaza

Ga Nijeriya, sakamakon wasannin da aka buga a Talatar nan ya nuna irin jan aikin da ke gaban Nijeriya kafin ta samu gurbi cikin waɗanda za su ƙare a mataki na biyu a rukuninsu.

Burkina Faso ta doke Sierra Leone da ci 1-0, Kamaru ta doke Mauritius da ci 2–0, sannan Madagascar ta ci Comoros 2–1, wanda ya sa suka ci makin da Nijeriya ba za ta iya kamo su ba.

A yadda ake ciki, Gabon da Madagascar suna da maki 19 kowannensu, yayin da Burkina Faso da Kamaru suke da maki 18 kowannensu.

Ko da Nijeriya ta ci duka wasanni biyu da suka rage mata, maki 17 kawai za ta iya samu.

Wannan na nufin dole Nijeriya ta ci duka wasanninta biyu, kuma ta ci su da tazarar ƙwallaye masu yawa. Sannan kuma ta yi fatan Afirka ta Kudu za ta ɓarar da maki.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#