Sport
Dollar
40,3762
0.14 %Euro
46,9005
0.06 %Gram Gold
4.331,2200
0.11 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya shaida wa Majalisar Ɗinkin Duniya cewa Gaza ya zama “sansanin musgunawa jama’a“, inda ya yi kira ga tsagaita wuta cikakkiya, da kuma kira da a bayar da damar kai kayan agaji.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Haka Fidan ya soki kisan kiyashin da Isra’ila ke aikatawa a Gaza a lokacin da yake jawabi a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya ce rikicin ya mayar da yankin zuwa ‘sansanin musgunawa jama’a’ inda ya zargi Isra’ila da tsara kai wa fararen-hula hare-hare.
“A yayin da muka taru a wannan zauren, kisan kiyashin da Isra’ila ke aikatawa kan Falasɗinawa na ci gaba babu ƙaƙƙautawa,” in ji Fidan a ranar Laraba.
“Fiye da mutane miliyan biyu na shan matsananciyar wahala a Gaza wadda ba a bayyana wa duniya.”
Ya ambato raba jama’a da dama da matsugunansu, rusau a wurare da yawa, da kuma toshe hanyoyin kai kayan agaji da gangan.
“Ana karkashe fararen hula a tare da bambance wa ba a wuraren karbar kayan taimako a yayin da suke kokarin karbar abinci da ruwa. Ana amfani da yunwa a matsayin makami a yakin,” in ji shi.
‘Makamai da aka gina da nuna tsana’
Fidan ya zargi isra’ila da karya duk wasu manyan ka’idoji na dokokin kasa da kasa.
“Babu bambanci ko yaro ne karami kai da ke dakko ruwa ko uwa da ke neman abinci - kawai Isra’ila za ta kashe ka,” in ji shi.
“Wannan makami ne da aka gina da tsana.”
Ya yi gargadin cewa rikicin jin kai a Gaza ya ta’azzara tare da zama wata jarrabawar halayyar ta duniya.
“Wasu sun zabi kawar da kawunansu. Ba za a ci gaba da aikata hakan ba.”
Ministan ya jaddada cewa Majalisar Dinkin Duniya ce kadai za ta iya tabbatar da an kai kayan taimako lami lafiya.
“Manyan ginshikan jin kan dan adam su ne, rungumar kowa,rashin daukar mangaranci da kuma ‘yanci, wadanda dole ne a kiyaye su.”
Hatsarin fadadar rikicin
Fidan ya kuma yi gargadin cewa yakin da sojojin Isra'ila ke yi na kawo hatsarin fadadar rikici a yankin.
“Wannan dabarar ta wuce gona da iri ta shafi Falasdinu kadai ba ne, har ma da Lebanon, da Syria da kuma Iran,” in ji shi.
"A Siriya, hare-haren Isra'ila na barazana ga kwarya-kwaryar zaman lafiya mai wahala."
Ya kuma bukaci kasashen duniya da su hana ruruwar wutar rikicin tare da tabbatar da cewa Syria ba za ta koma cikin rudani ba.
Fidan ta nanata goyon bayan Turkiyya don kafa cikakkiyar kasar Falasdina mai ‘yanci kuma mamba a Majalisar Dinkin Duniya.
"Wannan yana da mahimmanci don samun dauwamammen zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya," in ji shi.
A karshe ya yi kakkausar suka ga Kwamitin Tsaro na MDD.
"Ya gaza yi wa al'ummar Gaza komai. Ya kasa kare mutuncin bil'adama. Wannan ba kawai gaggawar ayyukan jin kai ba ce - gwaji ne na bil'adama baki daya."
"Abin da ya kamata a yi a bayyane yake karara: dakatar da injin yakin Isra'ila, dakatar da fin karfin fuskantar hukunci, tabbatar da tsagaita wuta nan da nan, da isar da kayan agajin jin kai ba tare da wata tangarda ba, da kuma sabunta alkawari kan samar da kasashe biyu-yanzu."
Comments
No comments Yet
Comment