Sport
Dollar
40,2579
0.12 %Euro
46,8671
0.37 %Gram Gold
4.332,1600
0.81 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A wata wasiƙa da Atikun ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Jada a jihar Adamawa, ya ce “Na rubuta wannan wasiƙa ne domin na ayyana ficewa ta daga jam’iyyar PDP a hukumance wacce ta fara aiki ba tare da ɓata lokaci ba.
Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP a 2023 ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
A wata wasiƙa da Atikun ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Jada a jihar Adamawa, ya ce “Na rubuta wannan wasiƙa ne domin na ayyana ficewa ta daga jam’iyyar PDP a hukumance wacce ta fara aiki ba tare da ɓata lokaci ba.
A wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Yulin 2025, Atiku ya ce yana gode wa jam’iyyar bisa damarmakin da ta ba shi na hidimta mata.
Ya ce ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasa sau biyu a ƙarƙashinta, kuma tsayawarsa takarar Shugaban Ƙasa sau biyu na daga cikin mafi muhimmanci a tarihin rayuwarsa.
“A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar nan, tabbas akwai ɗaukar wannan matakin abu ne mai nauyi.
“Kazalika, ya zama wajibi na dauki matakin ne saboda hanyar da jam’iyyar ta dauka a halin yanzu, wacce na yi imanin ta bambanta da ƙa’idojin da muka tsaya a kai.
“Na yi murabus ciki da nauyin zuciya, bayan fahimtar irin bambancen-bambancen da aka samu waɗanda ba za a iya sulhuntawa a kansu ba da suka bijiro.
A ƙarshen wasiƙar Atiku ya yi wa jam’iyyar da shugabancinta fatan alheri a nan gaba.
Comments
No comments Yet
Comment