Dollar

40,2481

0.1 %

Euro

46,8532

0.34 %

Gram Gold

4.335,8000

0.9 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A wani saƙo da ta wallafa a shafin X, kakakin Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta ambaci sunaye biyar na wasu ‘yan ƙasashen Vietnam, Jamaica, Laos, Cuba da Yemen waɗanda aka tuhuma da aikata muggan laifukan fyaɗe da kisan kai.

Amurka ta ce ta jibge ‘yan wasu ƙasashe da ta kora a ƙasar Estwatini da ke Kudancin Afirka

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka a ranar Talatar nan ta bayyana cewa wani jirgin sama ɗauke da waɗanda aka kora ‘yan ƙasashe daban-daban ya sauka a ƙasar Estwatini, a wani ɓangare na korar ‘yan gudun hijira zuwa wata ƙasar.

A ƙarshen watan Yuni, Kotun Ƙolin Amurka ta buɗe kofa ga gwamnatin Shugaba Trump da ta dawo da ayyukan tisa ƙeyar ‘yan gudun hijira zuwa wasu ƙasashen da ba nasu na asali ba don hana su fuskantar cutarwar da ka iya samunsu. Wannan mataki ya ba wa gwamnatin babbar nasara a gagarumin shirinta na korar ‘yan gudun hijira masu yawa.

“Jirgin sama zuwa ƙasa ta uku mai tsaro ya sauka a ƙasar Eswatini da ke Kudancin Afirka - Wannan jirgi ya ɗauki wasu mutane da saboda munin halayensu ƙasashensu na asali ma sun ce ba za su karɓe su ba,” in ji kakakin Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka Tricia McLaughlin a ranar Talata.

A farkon wannan watan, wani babban jami’i a gwamnatin Trump ya faɗa a wata takardar gwamnati cewa jami’an shige da fice na Amurka na iya tisa ƙeyar ‘yan gudun hijira zuwa ƙasashen da ba nasu na asali ba bayan ba su sanarwa cikin awanni da ba su wuce shida ba.

Dole ne Jami’an Shige da Fice na Amurka da Fasa Ƙauri su jira na aƙalla awanni 24 don tisa ƙeyar ‘yan gudun hijira zuwa ƙasar waje bayan sanar da su hakan, in ji bayanan da ke ɗauke da kwanan watan 9 ga Yuli masu ɗauke da sa hannun daraktan riƙo na hukumar, Todd Lyns.

Hukumar Shige da Fice da Fasa Ƙauri ta Amurka (ICE) na iya korar su, amma zuwa wata ƙasa da ba ƙasarsu ba tare da ba su sanarwa ta aƙalla awanni shida, in ji bayanan, matuƙar dai an ba wa mutumin da za a kora din damar magana da lauya.

Sun kuma ce za a iya tisa ƙeyar ‘yan gudun hijirar zuwa ƙasashen da suka yi alƙawarin ba za su cutar ko azabtar da su ba.

Sabon tsarin na ICE ya shawarci gwamnatin Trump cewa za ta iya yin gaggawa wajen aika ‘yan gudun hijirar zuwa ƙasashe daban-daban a faɗin duniya.

Masu rajin kare hakkokin ɗan’adam sun bayyana damuwa kan bin ƙa’ida da sauran batutuwa a manufofin da suka shafi gudun hijira na gwamnatin Trump da ke cewa ta ɗauki matakan ne don inganta tsaron cikin gida.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#