Sport
Dollar
39,1011
0.04 %Euro
44,4609
0.52 %Gram Gold
4.202,2600
1.92 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ana neman Kabila ruwa a jallo a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo saboda zargin goyon bayan ‘yan tawaye a gabashin kasar.
Majalisar dattawa ta Jumhuriyar ta amince da cire rigar kariyar tsohon shugaban kasar Joseph Kabila a wani zaman jefa kuri’a a yammacin Alhamis, saboda zargin sa da alaka da ‘yan tawayen M23.
Ana neman Kabila ruwa a jallo a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo bisa zargin aikata muggan laifuka kan bil’adama da goyon bayan ta’addanci a gabashin kasar, ciki har da zargin aikata kisan kiyashi ga farar hula.
Gwamnati na kuma kokarin dakatar da jam’iyyarsa tare da kwace kadarorin shugabanninta.
Kabila, wanda ya musanta yana da alaka da kungiyar ‘yan tawayen, ya yi murabus a 2018 bayan kwashe kusan shekaru 20 yana mulki. Tun karshen 2023 ya bar kasar ta Tsakiyar Afirka.
Majalisar dattawan ta amince da cire rigar kariyan bayan jefa kuri’u 88, inda wasu kuri’u biyar suka nuna rashin amincewa.
‘Yan tawayen M23
Kabila ya bayar da shawarar zai dawo Kongo tare da taimaka wa jen neman mafitar rikicin gabashin kasar, inda M23 ke rike d iko yanzu haka.
Washington na kokarin ganin an cim ma matsaya tsakanin bangarorin biyu a wannan bazarar, inda za a samu zuba jarin Yammacin duniya na biliyoyin daloli zuwa yankin, in ji Massad Boulos, babban mai baiwa shugaba Donald Trump shawara kan Afirka, ya fada wa Rueters a farkon wannan watan.
A 2001 Kabila ya hau mulki bayan an kashe mahaifinsa. Ya ki sauka daga mulki bayan wa’adinsa ya kare a 2016, inda aka samu mummunar zanga-zanga da rasa rayuka, inda a karshe a 2018 ya yarda ya sauka daga mulkin bayan an gudanar da zabe.
Comments
No comments Yet
Comment