Dollar

39,0309

0.28 %

Euro

44,0792

-0.04 %

Gram Gold

4.134,3600

0.27 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kirkirarriyar Basira na iya kawo babban sauyi a harkokin zabuka a Nijeriya, inda a daya bangaren kuma, ana iya amfani da shi wajen yada labaran karya, jirkita bayanai da aikata manuba a yanar gizo.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC za ta samar da sashen aiki da Ƙirkirarriyar Basira

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa a Nijeriya (INEC), a ranar Talatar nan 22 ga Mayun 2025, ta bayyana aniyar samar da wani sashe na aiki da Kirkirarriyar Basira a lokutan zabe da ma ayyukan da suka jibinci zabuka a Nijeriya da duniya baki daya.

A wata sanarwa da Hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun Kwamishinan Kasa kuma Shugaban Sadarwa da Wayar da Kan Masu jefa Kuri’a, Sam Olumekun, an bayyana cewa hukumar ta halarci manyan taruka a fadin nahiyar Afirka kan tasirin Kirkirarriyar Basira kan zabuka.

Sanarwar ta ce ba wai iya samuwar da ake da ita kan iya amfani da Kirkirarriyar Basira wajen yada labaran karya da jirkita bayanai a yanar gizo ne kadai suka sanya daukar matakin, har ma da bukatar amfani da basirar tattara bayanan wajen inganta ayyukan zabe, rarraba kayan aiki, daukar matakai, kawar da faɗawa hatsari da rage tasirinsa.

Sakamakon haka, INEC ta amince da kafa Cibiyar Kirkirarriyar Basira a karkashen Sashen Fasaha Sadarwa na Hukumar don ci gaba da amfana da Kirkirarriyar Basira da kuma kare harkokin zabe daga illatuwa da tsarin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa wannan sashe zai taimaka wa Hukumar ta INEC wajen yin kyakkyawan amfani da kayan aikin fasaha na zamani da take da su, sannan ya inganta duakar matakai da yanke hukunci, tare da habaka hulda da masu jefa kuri’a.

Kazalika sabon sashen zai karfafa inganci zabuka ta hanyar nazari kan alkaluma da kuma tsare basirar da ke aiki da kanta.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#