Dollar

39,0333

0.29 %

Euro

44,1780

0.29 %

Gram Gold

4.137,8300

0.35 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Turkiyya ta yi amanna cewa “Hoton iyalan duniyar Turkawa zai zama mai nakasu a ko yaushe idan babu Jumhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus a ciki,” in ji Erdogan.

Shugaban Turkiyya ya ce duniyar Turkawa ba za ta cika ba sai da Jumhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus

Shugaban Kasar Turkiyya ya ce Kungiyar Hadin Kan Kasashen Turkawa ba za ta cika ba matukar aka ce babu Jumhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus a cikin ta.

“Mun yi amanna hoton iyalan duniyar Turkawa zai zama mai nakasu a koyaushe idan babu Jumhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus a ciki,” in ji shugaba Erdogan a wajen taron kungiyar ta Turkic a Budapest a ranar Laraba.

A watan Nuwamban 2022, Jumhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus ta zama mamba ‘yar kallo a kungiyar,a wajen taron da aka gudanar a Samarkand.

Erdogan ya kuma kira “Hanyar Tsakiya” a matsayin hanya mai muhimmanci da ke tsakanin Gabas da Yamma, yana mai kira ga yin babban hadin kai a tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Da yake bayani game da rikicin baya da na yanzu da aka yi a yankin, ya ce “Bala’o’in da suka faru a baya a Cyprus, Karabakh, Bosnia, da Gaza a yau na tunatar da mu cewa dole ne mu kalli abubuwan da ke kwance a kan iyakokinmu.”

Game da yakin Ukraine da ake ci gaba da gwabzawa, Erdogan ya ce "Za mu ci gaba da tattaunawa sosai da dukkan kasashen biyu (Rasha da Ukraine) don ganin an samu tsagaita wuta da zaman lafiya”

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#