Dollar

39,0329

0.28 %

Euro

44,1574

0.24 %

Gram Gold

4.139,8100

0.4 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An yanke wa tsohon Firaministan DRC, Augustin Matata Ponyo, hukuncin daurin shekaru goma saboda "almundahana" da dala miliyan 247 mallakin gwamnatin ƙasar.

An yanke wa tsohon firaministan DRCCongo hukuncin daurin shekaru 10 kan cin hanci da rashawa

An yanke wa tsohon Firaministan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Augustin Matata Ponyo hukuncin ɗaurin shekaru goma a ranar Talata bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa.

Bayan shafe kusan shekaru huɗu ana taƙaddamar fara shari'a, kotun tsarin mulkin Congo ta samu Matata mai shekaru 60 da laifin wawure dukiyar al’umma da ta kai dala miliyan 247.

Matata, wanda ya fafata a yaƙin neman zaɓe da shugaban ƙasar na yanzu Felix Tshisekedi a zaɓen 2023 kafin ya sha kaye, ya yi ta musanta zargin da ake yi masa, yana mai bayyana su a matsayin farfagandar siyasa.

Baya ga Matata, alƙalin kotun Dieudonne Kamuleta ya yanke hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar tare da aikin ƙarfi ga wani ɗan kasuwa kana ɗan asalin kasar Afrika ta Kudu da kuma Deogratias Mutombo, wanda ya a lokacin shi ne gwamnan babban bankin ƙasar DR Congo.

An hana shi rike mukamin na tsawon shekaru biyar

An hana Matata da Mutombo rike mukaman gwamnati na tsawon shekaru biyar bayan sun kammala hukuncin da aka yanke musu, yayin da aka ba da umarnin a kori ɗan Afrika ta Kudu daga kasar ta DRC bayan ya gama wa’adin hukunci da aka ba shi.

Lauyan Matata, Laurent Onyemba, ya shaida wa AFP cewa akwai rashin ‘‘adalci’’ a hukuncin da aka yanke, kuma hakan shaida ce da ke nuna "wannan shari'ar siyasa ce."

 A yanzu shi ne shugaban jam'iyyar adawa ta Leadership and Governance for Development (LGD), Matata yayi aiki a gwamnatin Joseph Kabila daga 2010 har zuwa 2016, a farko a matsayin ministan kudi sannan kuma a matsayin firaiminista.

Lamarin dai ya fito fili ne a watan Nuwamban shekarar 2020, lokacin da hukumar IGF da ke sa ido kan kudaden da ake kashe wa a kasar ta bayyana cewa, an wawure dala miliyan 205 daga cikin dala miliyan 285 da aka sanya cikin wani shirin kafa masana'antu a Bukangalonzo mai tazarar kilomita 250 kudu maso gabashin babban birnin kasar.

‘Matata ya yi ikirarin cewa zarge-zarge ne kawai’

Hukumar ta IGF ta bayyana Matata a matsayin wanda ke kan gaba wajen aikata laifin, ikirarin da tsohon firaministan ya kira "zagi mara tushe".

 An fara sauraren ƙarar ne a watan Oktoban 2021, wanda ya yi sanyi bayan kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa ba ta da iko a kan tsofaffin firaiministocin ƙasar.

Daga nan kuma, a watan Yuni 2022 aka miƙa ƙarar zuwa wata kotu, wacce ke da hurumin shari’a kan 'yan majalisa.

Bayan wasu makonni, kotun ta mayar da batun zuwa Kotun Tsarin Mulkin ƙasa.

 Mara wa abokin hamayyar Tshisekedi a zaɓukan baya-bayan nan

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023 Matata ya fice daga takarar inda ya goyi bayan tsohon gwamnan lardin Moise Katumbi da fatan kawar da Tshisekedi, yana mai zargin gwamnatinsa da shirya "gagarumin maguɗin zaɓe."

 Tshisekedi ya sha alwashin mayar da yaƙi da cin hanci da rashawa a matsayin jigo a shugabancinsa, inda aka yanke wa wasu fitattun aminan Kabila hukunci a kan idon sa.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#