Dollar

40,1771

0.23 %

Euro

47,0764

0.07 %

Gram Gold

4.330,2600

1.08 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Muƙaddashiyar mai gabatar da ƙara ta Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Ƙasa da Ƙasa (ICC) Nazhat Shameen Khan ta yi gargaɗin cewa yunwa na ta’azzara a Sudan sakamakon yadda aka gaza kai kayan agaji ga mabuƙata.

Muƙaddashiyar mai gabatar da ƙara a Kotun ICC ta ce ana ci gaba da aikata laifukan yaƙi a Sudan

Akwai “manyan dalilai da za su sa a tabbatar da ana aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil’adama” a yaƙin da ya rikita yankin Yammacin Darfur da ke Sudan, in ji muƙadasshiyar mai gabatar da ƙara ta kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa (ICC).

Da take bayyana binciken da ofishinta ke yi kan yaƙin da ya ɓarke a 2023, Nazhat Shameem Khan ta shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya cewa “yana da wahala a iya samun kalmomin da za a yi amfani da su wajen bayyana munin rikicin Darfur.”

“Duba ga bincikenmu mai zaman kansa da muke yi, matsayar ofishinmu a bayyane take ƙarara. Muna da manyan dalilai da za su sanya a tabbatar da ana aikata laifukan yaƙi da ci gaba da cin zarafin bil’adama a Darfur,” in ji ta.

Khan ta ce binciken ofishin mai gabatar da ƙarar ya mayar da hankali kan munanan laifukan da ake aikatawa a Yammacin Darfur, inda waɗanda lamarin ya rutsa da su da aka tattauna da su ke guduwa zuwa Chadi.

Ta yi cikakken bayani kan ‘mummunan yanayin’ jinƙai, inda ake kai hare-hare kan asibitoci da jerin gwanon motocin agaji, inda ta yi gargaɗin “yunwa na ta’azzara” a yayin da ba a samun damar kai kayan taimako ga “waɗanda ke cikin tsananin buƙata”.

“Ana hana mutane samun ruwan sha da abinci. An mayar da fyaɗe da cin zarafi a matsayin makamai,” in ji Khan, tana mai ƙarawa da cewar garkuwa da mutane da neman kuɗin fansa sun zama ruwan dare.”

“Kuma kar mu yi tunanin wai abubuwa za su yi kyau, za su iya ƙara munana ne.”

Saboda dalilan kashe mutane

Kwamitin Tsaron ya alaƙanta yanayin Darfur na yanzu da na ICC a 2005, inda aka kashe mutane 300,000 a rikicin da aka yi a yankin a shekarun 2000.

A 2023, ICC ta fara binciken laifukan yaƙi a Darfur bayan rikici ya ɓarke tsakanin mayaƙan RSF da Rundunar Sojin Sudan.

An zargi mayaƙan Janjaweed da aikata laifukan kisan kiyashi shekaru 20 da suka gabata a yammacin ƙasar.

Ana sa ran alƙalan ICC za su yi hukuncin farko kan munanan laifukan da aka aikata a Darfur inda aka tuhumi Ali Mohamed Ali Abd-Al-Rahman da aka fi sani da Ali Kosheib, bayan kammala tuhumar a 2024.

“Ina son na bayyana ƙarara cewa ga wadanda ke cin karensu babu babbaka a yanzu a Darfur, da waɗanda suke azabtar da jama’a - a yanzu za su iya gagarar kowa, kamar yadda Ali Kosheib ya taɓa zama a baya,” in ji Khan.

Ta ƙara da cewa “Amma muna aiki sosai don tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Ali Kosheib ya zama misali na farko game da irin sa da dama da za a tuhuma a kotun ta ICC.”

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#