Sport
Dollar
40,2513
0.11 %Euro
46,8891
0.42 %Gram Gold
4.341,3800
1.03 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Harin na Isra’ila ya zo a yayin da take ci gaba da kai wa dakarun Syria hare-hare a kudancin garin Sweida.
Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai hari mashigar Hedkwatar Rundunar Sojin Syria da ke birnin Damascus.
“Dazun nan, Sojoji (na Isra’ila) suka kai hari ta sama kan hedkwatar rundunar sojin gwamnatin Syria a yankin Damascus na Syria,” In ji wata sanarwa da Isra’ila ta fitar a ranar Laraba.
Tashar talbijin ta Isra’ila ta rawaito cewa an jikkata mutane biyu a tsakiyar birnin Damascus, amma ba ta bayar da takamaiman wajen da lamarin ya faru ba.
Kazalika tashar ta bayar da labarin cewa an jiyo karar harbe-harbe a kusa da Hedkwatar Rundunar Sojin Syria.
Gidan rediyon Isra’ila ya tabbatar da kai harin inda ya ce a harin an nufi kayayyakin sojojin Syria.
Isra’ila ta sanar da cewa za ta aika da Karin sojoji zuwa iyakarta da Syria.
Harin ya zo ne jim kadan bayan Ministan Tsaron Isra’ila Katz ya yi barazanar ci gaba da kai wa sojojin Syria hare-hare idan ba su janye daga Sweida ba, wanda ke fuskantar rikici tsakanin jama’ar Druze da Bedouin.
Comments
No comments Yet
Comment