Dollar

38,7504

0.36 %

Euro

43,6473

0.26 %

Gram Gold

4.145,2800

1.01 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Babban attajiri a duniya, Bill Gates ya soki Elon Musk da gwamnatin Amurka ta Donald Trump kan zaftare kasafin kuɗin Amurka na tallafawa ƙasashen waje, inda ya zarge su da saka rayuwar miliyoyin rayuka a duniya cikin haɗari.

Bill Gates ya yi alkawarin ba da dala biliyan 200 nan da shekarar 2045

Attajirin Amurka Bill Gates ya yi alƙawarin bayar da kusan kacokan ɗin dukiyarsa ta ƙashin-kai cikin shekaru 20 masu zuwa, inda ya ce mafi talaucin mutane a duniya za su samu kimanin dala biliyan 200 ta hanyar gidauniyarsa.

Wannan shan alwashin na zuwa ne a lokacin da gwamnatocin duniya, kamar na Amurka ke rage tallafin ƙasa-da-ƙasa.

Haka kuma, Gates ya soki wani attajirin Amurka, Elon Musk, wanda shi ne mutum mafi arziƙi a duniya kuma wani muhimmin mutum a gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump.

Gates na zargin Musk da da "halaka yara mafiya talauci a duniya" saboda rage kasafin kuɗaɗen tallafin da gwamnatin Amurka ke bayarwa.

"Ganin mutum mafi arziƙi a duniya yana kashe yara mafi talauci a duniya ba kyakkyawan hoto ba ne," in ji Gates da yake magana da jaridar Financial Times.

Sashen Inganta Ayyukan Gwamnati da Musk ke jagoranta, ya assasa rusa Hukumar Taimakon Ƙasa-da-Ƙasa ta Amurka (USAID), wadda a baya ta bayar da biliyoyin daloli don tallafawa ayyuka kamar allurar rigakafi ga yara da kuma agajin abinci na gaggawa.

Gates da Musk sun taɓa amincewa kan rawar da masu arziƙi za su taka wajen bayar da dukiya, amma daga baya sun samu saɓani sau da dama.

Gates ya ce yana hanzarta shirye-shiryen raba dukiyarsa, kuma zai rufe Gidauniyar Gates a ranar 31 ga Disamba, 2045.

"Mutane za su ce abubuwa da yawa game da ni idan na mutu, amma na ƙuduri ganin ba a ce 'ya mutu yana da arziƙi' ba," in ji attajirin mai shekaru 69, wanda ya kafa kamfanin Microsoft, kuma mai bayar da tallafin ayyukan jin-ƙai.

"Akwai matsaloli masu yawa da ke buƙatar warwarewa, wanda hakan zai hana na riƙe dukiyata, bayan na san za a iya amfani da ita don taimakon mutane."

Sukar Trump

A cikin wata sanarwa da ke caccakar yanke tallafin da Trump ya yi tun dawowarsa mulki a watan Janairu, Bill Gates ya ce yana son taimakawa wajen dakatar da mutuwar jarirai, yara da mata daga cututtukan da za a iya magancewa, da kawo ƙarshen cututtuka kamar shan-inna, maleriya da masassara, da kuma rage talauci.

"Babu tabbas ko ƙasashen duniya masu arziƙi za su ci gaba da tsayawa tsayin-daka don talakawansu," in ji Gates, yana sukar yanke tallafi daga manyan masu bayar da tallafi ciki har da Birtaniya da Faransa tare da Amurka, wadda ita ce babbar mai bayar da tallafi a duniya.

Gates ya ce duk da cewa gidauniyarsa tana da kuɗi mai yawa, ba za a samu cigaba ba, ba tare da tallafin gwamnati ba.

Ya yaba da martanin da aka samu kan yanke tallafi a Afirka, inda wasu gwamnatoci suka sake tsara kasafin kuɗinsu, amma ya ce, a matsayin misali, ba za a kawar da shan-inna ba tare da tallafin Amurka ba.

Bill Gates ya bayyana wannan a bikin cika shekaru 25 na gidauniyarsa. Ya kafa wannan ƙungiyar tare da tsohuwar matarsa, Melinda French Gates, a shekarar 2000, kuma daga baya suka haɗa gwiwa da wani attajirin shi ma, wato Warren Buffett.

Ba da dala biliyan 100

Tun daga lokacin da aka kafa ta, gidauniyar ta bayar da tallafin dala biliyan 100, don taimakawa wajen ceton rayukan miliyoyi da tallafawa shirye-shirye kamar na ƙungiyar rigakafi ta Gavi ,da Asusun Duniya don Yaƙi da Cutar AIDS, da Tarin Fuka da Maleriya.

Za a rufe ta bayan ta kashe kusan kashi 99% na dukiyarsa ta ƙashin-kansa, in ji Bill Gates. A baya, masu kafa gidauniyar sun yi tsammanin za a rufe ta ne bayan mutuwarsu.

Gates, wanda aka ƙiyasta dukiyarsa a kusan dala biliyan 108 a yau, yana sa ran gidauniyar za ta kashe kusan dala biliyan 200 nan da 2045, inda jimillar adadin zai dogara kan kasuwanni da hauhawar farashi.

Gidauniyar ta riga ta zama babbar mai taka rawa a fannin kiwon lafiya na duniya, tare da kasafin shekara-shekara da zai kai dala biliyan 9 nan da 2026.

Ta fuskanci suka kan ƙarfin ikonta, da tasiri a fannin da babu mai saka masa ido, duk da tana da tasiri kan manyan cibiyoyi ciki har da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Bill Gates kansa ya fuskanci labaran ƙage kansa, da ƙarerayi, musamman a lokacin annobar COVID-19.

Gates ya yi magana da Shugaban Amurka Donald Trump sau da dama a watannin baya, kan muhimmancin cigaba da zuba kuɗaɗe a kiwon lafiya na duniya.

"Ina fatan sauran masu arziƙi za su yi la’akari da yadda za su iya hanzarta kawo cigaba ga talakawan duniya idan suka ƙara himma da girman gudunmawarsu, domin wannan hanya ce mai matuƙar tasiri don ceton al’umma," in ji Bill Gates.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#