Dollar

38,7337

0.29 %

Euro

43,5120

-0.12 %

Gram Gold

4.118,7700

0.36 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Prevost, wanda ya zama shugaban Cocin Katolika na 267, yana da sassaucin ra'ayi kuma yana da alaƙa da Fafaroma Francis tare da gogewa a limancin coci a Peru.

Robert Francis Prevost ne Ba'amurke na farko da ya zama Fafaroma

An zaɓi Robert Francis Prevost a matsayin fafaroma na farko daga ƙasar Amurka, kamar yadda Fadar Vatican ta sanar.

Prevost, wanda ya zama shugaban Cocin Katolika na 267, yana da sassaucin ra'ayi kuma yana da alaƙa da Fafaroma Francis tare da kwashe shekaru da dama yana limancin coci a Peru, kuma yanzu za a riƙa kiransa da suna Leo XIV.

Manyan limaman coci ne suka zaɓi fafaroman ranar Alhamis wanda zai shugabanci mabiya ɗarikar Katolika kimanin biliyan 1.4, inda suka aike da farin hayaƙi daga cocin Sistine Chapel a kwana na biyu na zaɓen, abin da ke alamta cewa an zaɓi sabon jagoran cocin.

Dubban mutane ne suka taru a St Peter's Square cheered, inda suka riƙa tafi suna zubar da ƙwalla a lokacin da suka a fitiwar farin hayaƙi, sannan aka riƙa kaɗa ƙararrawa a cocin St Peter's Basilica da sauran coci-coci a faɗin birnin Roma.

Dandazon mutane sun garzaya yankin cocin basilica, wadda aka ƙawata da jajayen dardumomi domin fafaroma na 267 ya yi jawabinsa na farko.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#