Matakan, waɗanda aka ɗauka bayan hukumomin lafiya sun tantance halin da cutar ke ciki, sun haɗa da hana ’yan ƙasar Saudiyya zuwa Kenya da kuma dakatar da bayar da dukkan nau’o’in biza ga matafiya daga ƙasar da ke Gabashin Afirka.
Ƙasar Saudiyya ta sanar a ranar Jumma’a da ɗaukar wasu ƙarin matakan kariya daga cutar Ebola, ciki har da dakatar da zirga-zirgar mutane zuwa Kenya da shigowa Saudiyya daga ƙasar, a cewar Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya (SPA).
Matakan, waɗanda aka ɗauka bayan hukumomin lafiya sun tantance halin da cutar ke ciki, sun haɗa da hana ’yan ƙasar Saudiyya zuwa Kenya da kuma dakatar da bayar da dukkan nau’o’in biza ga matafiya daga ƙasar da ke Gabashin Afirka.
Haka kuma, Saudiyya za ta hana shigowar matafiya daga Kenya, ciki har da waɗanda suka bi ta wasu ƙasashe, amma suka zauna a Kenya ko wasu ƙasashen da cutar Ebola ta shafa a cikin kwanaki 21 kafin zuwansu Saudiyya.
Matakan kariya
Ya zuwa yanzu, Kenya ta samu rahoton mutane tara da suka kamu da cutar Ebola, biyu daga cikinsu sun rasu.
SPA ta ce waɗannan takunkumai na daga cikin matakan kariya da Saudiyya ta fara ɗauka tun shekarar 2019, waɗanda ta ƙara tsaurara a watan Mayun bana domin kare matafiya daga ƙasashen da ke fuskantar barazanar barkewar cutar Ebola.
A watan Yunin bana, Saudiyya ta dakatar da zirga-zirga zuwa da shigowa daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Uganda da Sudan ta Kudu.
Ƙasar ta kuma ƙarfafa matakan kariya ga matafiya daga ƙasashen da ke makwabtaka da wuraren da Ebola ta shafa, ciki har da tantance lafiyar matafiya a wuraren shiga ƙasar, gudanar da binciken annoba da kuma samar da hanyoyin gaggauta ɗaukar matakin lafiya.
Ci gaba da sa ido
Hukumar Kiwon Lafiyar Jama’a ta Saudiyya, wadda aka fi sani da Weqaya, ta ce halin da lafiyar jama’a ke ciki a ƙasar yana da kwanciyar hankali, kuma hukumomi na ci gaba da sa ido a kai.
Ta ƙara da cewa hukumomin ƙasar na bibiyar yadda cututtuka ke yaɗuwa a yankin da ma duniya baki ɗaya, tare da haɗin gwiwar hukumomin da abin ya shafa wajen aiwatar da matakan kariya idan bukatar hakan ta taso.
Ebola cuta ce mai tsanani da ƙwayar cuta ke haifarwa, kuma tana yaɗuwa ta hanyar taɓa jinin wanda ya kamu da ita ko wasu ruwan jikinsa kai tsaye.
Cutar na iya haifar da zazzaɓi, amai, gudawa da kuma zubar jini a ciki ko wajen jiki a wasu lokuta masu tsanani.
TRT Afrika — TRT Afrika

