Dollar

38,6459

0.05 %

Euro

43,8506

-0.26 %

Gram Gold

4.201,5400

-1.5 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Sojojin Saman Pakistan sun harbo jiragen yaƙin India biyar bayan India ta kutsa cikin ƙasarsu inda ta kashe fararen-hula takwas tare da jikkata mutum 35, a cewar Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Asif.

Pakistan ta harbo jiragen yaƙin India biyar, ta yi garkuwa da sojojin ƙasar — Ma'aikatar Tsaro

Sojojin Saman Pakistan sun harbo jiragen yaƙin India biyar, kamar yadda kafofin watsa labaran gwamnati da na ƙasar Pakistan suka bayyana.

Sun ɗauki wannan mataki ne bayan India ta harba makamai masu linzami a cikin Pakistan lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas tare da jikkata aƙalla mutum 35 sannan mutum biyu sun ɓata.

Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Asif ya ce an harbo jiragen yaƙin India biyar kuma an yi garkuwa da sojojin India takwas a matsayin fursunonin yaƙi.

Tun da farko, Ministan Watsa Labaran Pakistan Attaullah Tarar ya shaida wa TRT World cewa an harbo jirgi guda ɗaya a birnin Akhnoor da ke yankin Kashmir wanda ake taƙaddama a kansa, sannan aka harbo wani jirgin a birnin Ambala na ƙasar India, kazalika an harbo jirgi marasa matuƙi a lardin Jammu na ɓangaren Kashmir da ke ƙarƙashin ikon India.

Tarar ya ƙara da cewa sojojin Pakistan sun mayar da martani ne kan harin da India ta kai ƙasar da makamai masu linzami waɗanda ta harba a yankunan "fararen-hula".

Wani mai magana da yawun rundunar sojojin Pakistan ya ce sun “lalata” wasu kayayyakin tsaron India.

Mazauna yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon India sun ce sun ji ƙararraki masu ƙarfi sannan suka riƙa yaɗa bidiyoyin wasu sassan jiragen sama da aka harbo.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#