Sport
Dollar
38,5992
0.33 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.017,2800
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hukumar Hana Faruwar Bala'o'i da Bayar da Agajin Gaggawa ta Chile ta ba da umarnin ficewa daga yankin gaɓar ruwan Antatika da Yankin Magallanes.
Wata girgizar ƙasa mai ƙarfi da ke da ma’aunin 7.4 ta afku a kudancin gabar tekun Chile da Argentina, kamar yadda Hukumar Binciken Ƙasa ta Amurka (USGS) ta bayyana.
Hukumomin Chile sun bayar da sanarwar gaggawar fitar da mutane daga dukkan yankunan bakin teku a Mashigin Magellan a kudancin ƙasar a ranar Jumma’a.
Girgizar ƙasar ta faru ne kusan kilomita 219 (mil 136) kudu da Argentina da ƙarfe 12:58 agogon GMT, kuma ta kai zurfin kilomita 10, kamar yadda binciken farko na hukumar ya nuna.
Hukumomin Argentina ba su bayar da rahoton asarar rayuka ko lalacewar dukiya ba nan take.
Duk da haka, Hukumar Nazarin Tekuna da Ruwa ta Chile (SHOA) ta ƙiyasta girman girgizar ƙasar a ma’aunin 7.8, tana mai bayyana cewa ta faru kilomita 305 kudu da Puerto Williams, tare da bayar da gargaɗin yiwuwar ambaliyar tsunami ga yankunan da ke bakin teku.
A matsayin matakin kariya, Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa ta Chile (SENAPRED) ta umarci a fitar da mutane daga bakin teku a yankin Antatika da Magallanes.
Shugaban Chile, Gabriel Boric Font, ya yi kira ga mazauna yankin su bi umarnin hukumomi, inda ya bayyana a X cewa: “Muna kira ga mutane su fita daga bakin teku a duk faɗin yankin Magallanes. Ayyukanmu shi ne mu kasance cikin shiri kuma mu saurari hukumomi.”
Comments
No comments Yet
Comment