Dollar

38,6001

0.08 %

Euro

43,7775

0.2 %

Gram Gold

4.177,6100

1.05 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Erdogan ya ce sun jaddada cewa alaƙar da ke tsakaninsu za ta bunƙasa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannin tsaro da cinikayya.

Erdogan ya yi magana ta wayar tarho mai 'armashi kuma cikakkiya' da Trump

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce maganar da ya yi ta wayar tarho da shugaban Amurka Donald Trump "mai matuƙar armashi ce kuma mai faɗi, sannan cike da bayyana gaskiya."

" Wayar tarho da muka yi a yau tare da babban abokina Shugaba Donald Trump ta kasance mai armashi kuma a bayyane, cikin gaskiya," in ji Erdogan a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin bayan sun kammala magana a wayar tarho.

"Ina fatan ganawa da abokina Trump nan ba da jimawa ba," a cewar Erdogan, wanda ya bayyana fatan ganin cewa ganawar za ta kasance mai "alheri ga ƙasashenmu."

Erdogan ya ce sun jaddada dangantaka tsakanin ƙasashensu, yana mai fatan matakin zai kyautata alaƙa a fannoni daban-daban, musamman a fannin tsaro da cinikayya.

Shugabannin biyu sun tattauna a kan batutuwa daban-daban, ciki har da alaƙa tsakanin Turkiyya da Amurka, da harkokin da suka shafi yankinsu da ma duniya baki ɗaya.

Da yake magana game da matsalar rashin jinƙai a Gaza, Erodogan ya ce lamarin ya yi ƙarami kuma akwai buƙatar a riƙa kai kayan agaji ba tare da katsewa ba.

Haɗa kai domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa

A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Erdogan goyi bayan matakin Trump na kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe da kuma jinjina masa game da yin sulhu da Iran da yunƙurinsa na kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine.

"Na nuna goyin bayana da kuma jinjina ga Shugaba Trump bisa yunƙurinsa na kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a duniya, kuna na jaddada matsayin Turkiyya na kasancewa a shirye domin bayar da dukkan gudunmawar da ta dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankinmu," in ji shi.

"Na bayyana cewa zan yi matuƙar farin ciki na karɓi baƙuncin abokina a Turkiyya a kowane lokaci nan kusa, kuma shi ma, ya gayyace ni zuwa Amurka," a cewarsa.

Erdogan ya jaddada matsayin Turkiyya a yunƙuri na tabbatar da kasancewar Syria a matsayin ƙasa mai 'yancin kanta da samar da zaman lafiya. Ya ce yunƙurin Amurka na sassauta takukunkumai kan Syria zai taimaka wajen wannan tsari.

Kazalika Shugaba Erdogan ya gayyaci Trump domin kai ziyara Turkiyya.

Trump ya bayyana tattaunawar a matsayi "mai matuƙar armashi" kuma ya ce yana fatan yin aiki tare da shugaban Turkiyya domin kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine.

Haka kuma ya ce Erdogan “zai zo Washington, DC”.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#