Mohammed Azraq al-Fanjari ya ce haka kuma motocin yaƙi 30 sun bar mayaƙan na RSF.

Babban kwamanda a mayaƙan RSF ya koma rundunar sojin Sudan tare da mayaƙa 300

Wani kwamanda a rundunar mayaƙan sa-kai ta RSF ya sanar a ranar Alhamis cewa ya ɓalle daga ƙungiyar tare da mayaƙa 300 da motocin yaki 30.

Mohammed Azraq al-Fanjari, kwamandan rundunar ayyuka na musamman ta RSF, ya sanar da ficewarsa ne ta cikin wani saƙon bidiyo da aka watsa a kafofin yaɗa labaran Sudan.

Al-Fanjari ya ce ya yanke shawarar ajiye dukkan ayyukansa da nauyin da ke kansa a cikin RSF "bayan yin nazari na gaskiya a kanmu da kuma zurfin tunani game da halin da ƙasarmu ta tsinci kanta a ciki sakamakon wannan yaƙin da ba shi da amfani."

Ya ce ya fi fifita "darajar rayuwar ɗan Sudan da kuma zaɓin zaman lafiya."

Ba da hakuri ga iyalai

Har ila yau, Al-Fanjari ya bayyana cewa ba shi da hannu wajen duk wani cin zarafi ko take haƙƙin fararen hula ko dukiyoyinsu, kuma ya ba da hakuri ga iyalai a Sudan da wannan rikici ya shafa ta hanyar mutuwa, ko gudun hijira, ko wasu illoli tun bayan ɓarkewarsa a watan Afrilun 2023.

Ya yi kira ga sauran mambobin ƙungiyar da su sake duba matsayinsu su kuma fita daga ƙungiyar, inda ya bayyana rikicin a matsayin "yaƙi mara dalili kuma mara makoma."

Kwamandan ya buƙaci tsoffin abokan aikinsa su goyi bayan Rundunar Sojin Sudan tare da ƙaurace wa ci gaba da zubar da jini.

#