Wannan shi ne rukuni na baya-bayan nan da ya isa ƙasar mai fama da talauci cikin watanni huɗu da suka gabata, sakamakon tsauraran matakan da Shugaban Amurka Donald Trump ke ɗauka kan shige da fice, waɗanda suka janyo ce-ce-ku-ce.
Wasu ’yan gudun hijira 25 da Amurka ta kora sun isa ƙasar Liberia da ke yammacin Afirka, kamar yadda wani kwamiti a ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Asabar.
Wannan shi ne rukuni na baya-bayan nan da ya isa ƙasar mai fama da talauci cikin watanni huɗu da suka gabata, sakamakon tsauraran matakan da Shugaban Amurka Donald Trump ke ɗauka kan shige da fice, waɗanda suka janyo ce-ce-ku-ce.
A baya-bayan nan ne gwamnatin Liberia ta sanar da cewa za ta karɓi baƙi daga ƙasashen waje har 1,200 a cikin shekara guda.
Wani jami’in wata hukumar Liberia da ke kula da harkokin ‘yan gudun hijira da samar musu matsuguni da walwala ya ce mutanen 25, ciki har da mata biyu, sun isa ƙasar ne da misalin ƙarfe 9:35 na ranar Juma’a a dare, agogon ƙasar.
Ya ƙara da cewa yawancin mutanen sun fito ne daga ƙasashen Kudancin Amurka, amma bai bayar da ƙarin bayani ba.
Liberia ta shiga jerin ƙasashen Afirka da suka amince su karɓi mutanen da Amurka ke kora daga ƙasarta. Sauran ƙasashen sun haɗa da Saliyo, Equatorial Guinea, Ghana, Rwanda, Sudan ta Kudu, Kamaru, Eswatini da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC).
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin yarjejeniyoyin sun haɗa da tallafin kuɗi ko na kayan aiki daga Amurka.
Sai dai gwamnatin Liberia ta taɓa bayyana cewa ba ta nemi ko karɓi wata diyya ko alƙawarin lada ba a madadin amincewarta da shiga shirin mayar da waɗannan mutane.
Duk da haka, jaridar New York Times ta ruwaito cewa Amurka ta biya Liberia dala miliyan biyar, bisa wasu takardu da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta amince da su, sakamakon alƙawarin Liberia na yin la’akari da karɓar mutanen da aka kora.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: AFP (Wire)

