Sport
Dollar
41,3196
0.09 %Euro
49,0491
0.51 %Gram Gold
4.870,5500
0.28 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%“Ana garkuwa da yawancin waɗannan ‘yan matan ne domin neman kuɗin fansa da auren dole da kuma musayar fursunoni,” a cewar Nahla Haidar, shugabar kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wani kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya mai lura da wariya kan mata (CEDAW) ya ce aƙalla ɗalibai 1,400 aka yi garkuwa da su a Nijeriya tun bayan da ƙungiyar Boko Haram ta sace ‘yan matan Chibok a 2014.
Wata sanarwa da ofishin kare haƙƙin bil’adama na MDD ya fitar ta ce mambobin kwamitin na MDD sun bayyana haka ne bayan sun kai ziyarar mako biyu ta gani da ido Nijeriya a ɓoye a watan Disamba na shekarar 2023.
“Sace ‘yan matan Chibok ba ita ce bala’i ɗaya tilo da ya auku ba, ta kasance wani ɓangare na jerin sace-sacen mutane da ake yi a makarantu da da al’ummomi a faɗin arewacin Nijeriya, duk da cewa ita ce wadda aka fara yayatawa da ta samu goyon bayan duniya,” kamar yadda sanarwar ta ambato shugabar kwamitin na MDD, Nahla Haidar tana cewa.
“Duk da cewa hare-haren sun fara ne daga farko, abin da ya faru a Chibok shi ne lokacin da duniya ta fara mayar da hankali kan yanayin garkuwa da mutane da yawa da aka shafe fiye da shekara goma ana yi. An yi garkuwa da ɗalibai aƙalla 1,400 daga makarantunsu tun bayan satar ‘yan matan Chibok,” in ji shugabar kwamitin ta CEDAW.
“Yawanci ana garkuwa da waɗannan ‘yan matan ne domin neman kuɗin fansa da auren dole da kuma musayar fursunoni,” a cewar Nahla Haidar.
Comments
No comments Yet
Comment