Sport
A farkon makon ne Ministan Lafiya na Kasar Farfesa Mohammed Ali Pate ya koka kan naira miliyan 36 da aka bai wa ma’aikatarsa daga cikin naira biliyan 218 da aka ware mata a kasafin kudin shekarar 2025.
Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Tarayya a Nijeriya suna ƙorafi cewa ba a sakar musu kuɗaɗen da aka ware a kasafin kudin ƙasar don gudanar da manyan ayyukan ci gaban kasa ba.
A farkon makon ne Ministan Lafiya na Kasar Farfesa Mohammed Ali Pate, yayin zaman kare kasafin kudin Ma’aikatar Lafiya na shekarar 2026 a zauren majalisar dokokin kasar, ya yi korafin cewa ko da yake an bai wa ma’aikatar duka kudin da aka ware na bangaren albashin ma’aikata, amma kuma ya koka kan naira miliyan 36 da aka bai wa ma’aikatarsa daga cikin naira biliyan 218 da aka ware mata a kasafin kudin shekarar 2025.
Kazalika Mukaddashin Shugaban Hukumar Dillancin Lantarki a Nijeriya wato Nigerian Bulk Electricity Trading (NBET) Plc, Johnson Akinnawo ya shaida wa majalisar dattawan kasar cewa naira miliyan 60 kacal aka bai wa hukumarsa daga cikin biliyan 858 na manyan ayyuka da aka ware wa hukumar a cikin kasafin kudin shekarar 2025.
Mista Akinnawo ya bayyana haka ne lokacin da ake zaman bitar kasafin kudin bara da kuma kare kasafin kudin hukumar na bana a gaban kwamitin kudin na majalisar dattawan kasar.
Tun bayan haka ’yan kasar suka fara bayyana ra’ayoyinsu musamman a kafafen sada zumunta.
Fitaccen dan jarida kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Rufai Oseni ya wallafa a shafinsa na X cewa ya kasa yin barci tun bayan da Ministan Lafiya Farfesa Pate ya bayyana cewa naira miliyan 36 kacal aka bai wa ma’aikatarsa don gudanar da manyan ayyuka a shekarar da ta gabata.
Daraktan Kungiya Mai Inganta Ayyukan Majalisu (CISLAC) kuma jagoran Kungiya Mai Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Transparency International a Nijeriya Malam Auwal Musa Rafsanjani ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa da farko dai kasafin kudi doka ce da zarar an sanya masa hannu.
Ya jaddada cewa kasafin kudi doka ce kamar sauran dokokin kasa, yana mai cewa ƙin aiwatar da kasafin kudi yadda ya kamata take dokar kasa ne musamman kasancewa yanzu ana magana ne kan aiwatar da kasafin kudin ma’aikatar kiwon lafiya.
Rafsanjani ya ce Nijeriya tana daya daga cikin kasashen Afirka da suka sanya hannu kan cewa ta amince za ta riƙa ware kaso 15 cikin 100 na kasafin kudin kasar wajen kula da harkokin kiwon lafiya.
Ya ce shekaru sun wuce har yanzu ba a ko kama kafar aiwatar da wannan adadi a fannin kiwon lafiyar kasar ba.
Ya ce dole ne idan kasa tana so ta ci gaba, to wajibi ne sai ta inganta fannin kiwon lafiyar al’ummarta saboda haka ya ce ƙin bai wa ma’aikatar lafiya kudin da aka ware mata a kasafin kudi koma baya ne sosai ga ci gaban ƙasa, kuma a cewar Rafsanjani hakan ba zai haifar wa Nijeriya alheri ba.
Comments
No comments Yet
Comment