Sport
Dollar
38,8949
0.36 %Euro
43,4533
-0.25 %Gram Gold
3.997,1000
-0.9 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban kamfanin BUA ya yaba wa Shugaba Bola Ahmad Tinubu kan damar shigowa da abinci da ya bayar, inda ya ce “hangen nesansa” ya taimaka wajen karya farashin abinci a ƙasar.
Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yi alƙwarin ƙara karya farashin shinkafa da sauran kayayyakin abinci duk da cewa farashin ya sauƙa cikin shekarar da ta gabata.
Ya yaba wa Shugaba Bola Ahmad Tinubu kan damar shigowa da abinci da ya bayar, yana mai cewa “hangen nesansa” ya taimaka wajen karya farashin abinci a ƙasar.
A cikin watan Yulin shekarar 2024, gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi shelar dakatar da karɓar haraji kan kayayyakin abincin da ake shigarwa ƙasar domin rage hauhawar farashin kayayyakin abinci.
Da yake magana da manema labarai bayan ya gana da Shugaba Tinubu ranar Alhamis, Rabiu ya ce kamfaninsa na BUA ya shiga cikin shirin gwamantin Tinubu na shigowa da abincin kuma ya yi nasarar shigowa da alkama da masara da shinkafa mai yawa.
“Farashin abinci ya yi tsada sosai a bara. Alal misali ana sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 kan kuɗi kimanin naira 100,000. Shi kuma buhun fulawa ana sayar da shi kan kimanin naira N80,000 inda ake sayar da rabin buhun masara kan kuɗi naira N60,000 kuma katan ɗin taliya kan kuɗi N20,000. Saboda haka abin da muka yi shi ne mun shiga cikin shirin kuma BUA ya samu ya shigo da alkama da masara da shinkafa mai yawa.
“Kuma bayan an fara jigilar abinci, muka fara sarrafa su. Mun karya farashin wasu daga cikin waɗannan kayayyakin abincin. Kuma a yau na yi murnar sanar da kai cewa farashin shinkafa yanzu kimanin naira N60,000 ne daga daga kimanin naira N110,000 da ya ke a bara. A yau buhun fulawa mai nauyin kilogiram 50 farashinsa ya koma naira N55,000.
“Rabin buhun masara kimanin naira N30,000 ne. Kuma wannan ya faru ne saboda hangen nesan shugaban ƙasa inda ya ba da damar shigowa da masara na watanni shida. Wannan ya sa mun samu mun karya farashin waɗannan kayayyakin,” in ji Rabiu.
Comments
No comments Yet
Comment