Kwamitin ba da kyautar Nobel na Norway ya yaba wa gomman shekaru da Pillay ta shafe tana ƙarfafa adalci a duniya da kuma tabbatar da cewa an tuhumi waɗanda suke aikata laifukan yaƙi da laifuka kan bil Adama da kuma kisan ƙare dangi.

'Yar Afirka ta Kudu Navi Pillay ta ci kyautar Nobel ta Zaman Lafiya ta shekarar 2026

‘Yar Afirka ta Kudu Navi Pillay, wadda ta jagoranci wata hukumar binciken Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) da ta tabbatar da cewa Isra’ila ta tafka kisan ƙare dangi a Gaza, ta samu kyautar Nobel ta zaman lafiya ta shekarar 2026 a ranar Jumma’a bisa gudumowar da ta bayar ga zaman lafiya da dokar ƙasa da ƙasa.

Kwamitin ba da kyautar Nobel na Norway ya yaba wa gomman shekaru da Pillay ta shafe tana ƙarfafa adalci a duniya da kuma tabbatar da cewa an tuhumi waɗanda suke aikata laifukan yaƙi da laifuka kan bil Adama da kuma kisan ƙare dangi.

"Mai kyautar noble na wannan shekarar ta faɗaɗa hanyar tasiri a dokar ƙasa da ƙasa," kamar yadda kwamitin ya bayyana, yana mai bayyana aikinta a kan kotunan ƙasa da ƙasa yayin da kuma matsayinta na kwamishiniyar ‘yancin bil Adama na MƊD.

An haife ta a ƙarƙashin mulkin wariyar launin fata

An haife ta ne a cikin wani iyali na asalin Tamil daga Indiya a Durban, na Afirka Ta Kudu South Africa, a ƙarƙashin mulkin wariyar launin fata, Pillay ta fara aikinta na shari’a ne inda take ƙalubalantar wariyar launin fata da kuma kare waɗanda ke adawa da tsarin wariyar launin fata na apartheid.

Daga baya a ta yi aiki a matsayin maishari’a a babban kotun AFirka ta Kudu da Kotun ƙasa da Ƙasa na Rwanda da kuma Kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa, kafin ta zama babbar kwamishiniya ta ‘yancin bil Adama ta MƊD.

Kwamitin ba da kyautar Nobel ta bayyana gudumowarta ga muhimman hukunce-hukunce da suka tabbatar da cewa fyaɗe da tsangwama na jima’i za su iya kasancewa laifuka kan bil Adama.

Pillay ta kuma yi aiki a matsayar alƙaliya na wucin gadi wa kotun ƙasa da ƙasa a ƙarar da gambia ta shigar kan Myanmar bisa zarge-zargen kisan kiyashi kan ‘yan tsiraru ‘yan ƙabilar Rohingya.

Binciken MƊD a Gaza

Pillay ce ta jagoranci hukumar binciken ƙasa da ƙasa na MƊD kan ƙasar Falasɗinun da aka mamaye daga watan Yulin shekarar 2021 zuwa lokacin da ta bari a shekarar 2025.

A lokacin da take gabatar da abubuwan da hukumar ta gano ga wani kwamitin Babban Zauren MƊƊ a watan Oktoban shekarar 2025, ta ce nazarin dokar da ta yi ta tabbatar da alhaƙin Isra’ila kan kisan kiyashi a Gaza.

"Mun gano cewa ƙasar Isra’ila ce ke da alhaƙin aikata aika-aikar kisan ƙare dangi a Gaza da zummar hallaka Falasɗinawa a Gaza, kamar haka," in ji ta.

"Hukumar ta kuma gano cewa Shugaban Isra’ila da Firayim Ministarta da ministan ma’aikatar tsaronta sun tunzura aikata kisan ƙare dangi," in ji ta.

'Muhimmancin hukumomin shari’a'

Kwamitin ba da kyautar Nobel ɗin ya ce aikin Pillay ya nuna muhimmancin hukumomin sharia na ƙasa da ƙasa wajen hana rikici da kuma tabbatar da fayyace gaskiya.

"Wajen bayar da kyautar Nobel ta Zaman Lafiya ta wanna shekarar, kwamitin ba da kyautar Nobel na Norway yana so ya tuna wa duniya cewa jagorancin doka -- na cikin ƙasa da na ƙasa da ƙasa -- su ne ginshiƙin tsrain da muka kafa domin tabbatar da zaman lafiya da kuma warware rikici ba tare da tashin hankali ba. Zamna lafiya na buƙatar adakci," in jikwamitin.

#