Rahotanni daga ƙasar da ke Yammacin Afirka sun ce ayyukan da rundunar ta ƙaddamar sun yi silar daƙile safarar miyagun ƙwayoyi masu yawa.
A wani ɓangare na burinta na tabbatar da tsaron mutane da kadarorinsu, da kuma yaƙar safarar miyagun ƙwayoyi rundunar tsaron ƙasa ta Nijar (GNN) ta yi nasarar kama mutum bakwai bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi da kuma ƙwace ƙwayoyi masu yawa.
Rahotanni daga ƙasar da ke Yammacin Afirka sun ce ayyukan da rundunar ta ƙaddamar sun yi silar daƙile safarar miyagun ƙwayoyi masu yawa.
Rahotannin sun ce rundunar GNN ta ƙaddamar da ayyukan ne tsakanin ranar 15 ta watan Satumba zuwa ranar 18 ta watan Nuwamban shekarar 2026, inda ta yi nasarar kama mutum bakwai waɗanda akasarinsu masu safarar miyagun ƙwayoyi da masu fasa ƙwauri ne.
Ayyukan sun kuma yi silar ƙwace ƙwayoyin magani 349,905 da ƙwayoyi masu sa maye da miyagun magunguna, ciki har da magungunan da aka haramta amfani da su, Royal/Tramadol da Tramaking da kuma Eskazepam.
Kazailka kafar Actu Niger ta ruwaito cewa rundunar ta ƙwace ƙwallaye 29 na tabar wiwi da nauyinsu ya kai kilogiram 24.024 da kara 31 da ke jiran sha.
Rundunar GNN ta kuma kama kwalaye 559 da sigari samfurin Yes guda 4 da kuma kwalayen juis da aka haramta.
Kazalila rahotannin sun ce samamen da rundunar ta kai a cikin wannan lokacin sun yi silar kama motoci biyar samfurinm Toyota V8 da babur ɗaya da amalanke ɗaya da kuma kuɗi 184,230 FCFA.
Rundunar GNN ta ce ta miƙa waɗanda ake zargin ga ofishin da ke yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi (OCRTIS) da kwastom, in ji rahotannin.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: National Guard (Niger)

