A cewar sojojin, hare-haren sun kuma lalata wani gini da ake zargin ’yanta’adda na amfani da shi a matsayin wurin shirya hare-hare, tare da daƙile shirye-shiryen ‘yanta’addan na kai hare-haren bama-baman da ake iya tayarwa ta na’ura.
Sojojin Nijeriya sun ce hare-haren sama da rundunar sojin sama ta Operation HADIN KAI ta kai sun yi sanadin kashe ’yanta’adda 37 tare da lalata motoci huɗu a yayin wani farmaki da ya ɗauki tsawon mako guda ana kaiwa a wurare daban-daban na Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da rundunar haɗin gwiwa ta musamman ta Arewa maso Gabas ta fitar a ranar 23 ga Nuwamba, ta ce an kai hare-haren sama guda shida bisa bayanan sirri a wurare biyar tsakanin ranakun 16 zuwa 23 ga Nuwamba, inda aka kai hari kan maboyar ’yanta’adda, zirga-zirgarsu da wuraren da suke ajiye kayayyakin tallafi.
Ayyukan sun shafi ƙaramar hukumar Monguno, da Kerenoa da Fage a ƙaramar hukumar Marte, da kuma yankin Tumbuma Baba na ƙaramar hukumar Kukawa.
A cewar sojojin, hare-haren sun kuma lalata wani gini da ake zargin ’yanta’adda na amfani da shi a matsayin wurin shirya hare-hare, tare da daƙile shirye-shiryen ‘yanta’addan na kai hare-haren bama-baman da ake iya tayarwa ta na’ura.
A wani hari da aka kai ranar 16 ga Nuwamba, an kashe ’yan ta’adda 10 da ake zargin sun nufi wurin dakarun soji da ke kusa da Monguno. A ranar 17 ga Nuwamba kuma, wani harin sama ya lalata wani gini a Arina Chiki, inda ake zargin mayakan na shirin kai hari kan sansanonin soji.
A ranar 20 ga Nuwamba, an lalata motoci biyu a Kerenoa, yayin da aka lalata wata motar a Fage, a wani wurin da ake zargin ana haɗa bama-bamai.
Sojojin sun ce a wani hari da suka kai ranar 23 ga Nuwamba, sun lalata motar ’yanta’adda a Tumbuma Baba. An kuma kashe wasu mutum takwas da ake zargin mayaka ne, waɗanda suka taru a kusa da wurin, a wani hari na sama da aka kai daga baya.
Rundunar Operation HADIN KAI ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare tare da dakarun ƙasa, inda ta yi kira ga mazauna yankin da su riƙa bayar da sahihan bayanai domin taimaka wa ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci a Arewa maso Gabas.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Others

