Dollar

40,6014

0.01 %

Euro

46,5754

0.43 %

Gram Gold

4.292,7000

0.44 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Isra'ila na ci gaba da ƙone-ƙone da mamaya, da kai hare-hare kullun a kan mazauna ƙauyen Kiristoci na ƙarshe a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye.

Yahudawa 'yan kama wuri zauna sun kai mummunan hari kan wani ƙauyen Falasɗinawa kiristoci

Mazauna garin Taybeh, wanda shi ne ƙauyen Kiristoci na karshe a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, sun ce an sha fama da hare-haren wuce gona da iri na Isra'ila a cikin 'yan makonnin da suka gabata, inda aka yi ta samun gobara, da barnar dukiya, da kuma kutsawa cikin yankin.

Da yake magana da kafar yada labarai ta Vatican a ranar Juma'a, dan fafutukar Kirista Bafalasdine Ihab Hassan, wanda dan asalin birnin Ramallah ne da ke kusa, ya bayyana yadda tashe-tashen hankula suka barke a kauyen mai yawan al’umma kusan 1,300.

A daren ranar 25 ga watan Yuni, an cinna wuta kusa da kofar Taybeh.

Makonni kadan bayan haka, wata gobara ta sake tashi a kusa da rusasshen Cocin St. George tun na ƙarni na 5.

Mazauna yankin da limaman cocin sun dora alhakin faruwar lamarin a kan wasu ‘yan Isra’ila da suka yi ƙaura ba bisa ka’ida ba, kuma Hassan ya tattara tare da yada bidiyo ta intanet don goyan bayan ikirarin nasa.

"Hare-haren ta'addanci da mazauna yankin ke kaiwa ba sabon abu ba ne," in ji Hassan, ya kara da cewa tuni rikicin ya tilasta wa iyalai kusan 10 barin kauyen.

"Kwanan nan," in ji shi, "tashin hankali ya karu, kuma ana kai hare-hare akai-akai, a kullum" a kauyukan da ke kewaye da Taybeh."

A ranar 25 ga watan Yuni, a cewar Hassan, wasu ‘yan kama wuri zauna na Isra'ila sun kai hari a kauyen Kafr Malik da ke kusa, inda suka kashe Falasdinawa uku.

Hotunan da Hassan ya yada sun nuna yadda maharan ke tafiya zuwa Taybeh, inda aka ƙona motoci a bakin kauyen.

An ci gaba da kai hare-hare, kamar yadda mazauna garin suka ce, inda aka ba da rahoton cewa wasu Yahudawa ‘yan kama wuri zauna Isra'ila sun yi ta kora shanu zuwa wata kasa mai zaman kanta a Taybeh.

"A zahiri sun mamayi mazaunan wadannan mutane," Hassan ya shaida wa Vatican News.

"Ya ce a wasu lokutan rikicin Yahuadawa ‘yan kama wuri zaunan da hujja suke yi, sai dai rashin adalci ne cewa martani ne ga zaluncin Falasdinu," in ji shi.

"Game da Taybeh," in ji shi, "ba zai yiwu a yi irin wannan uzuri ba. 'Kauyen Taybeh na Kirista ya kasance gari mafi kwanciyar hankali a duk yankin," in ji shi. "Waɗannan mutane ne masu zaman lafiya da ƙaunar juna."

Hassan ya kara da cewa, "‘Yan kama wuri zauna ne masu tsattsauran ra'ayi," in ji Hassan, yana mai cewa "jami'an Isra'ila da yawa suna goyon bayan hakan."

Ya yi nuni da cewa, wasu daga cikin wadanda ke da hannu a ciki sun kasance masu tsatsauran ra'ayi ta yadda hatta tsohon Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant, wanda kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta tuhume shi da aikata laifukan yaki, a baya ya sanya taɓa tsare su.

Sojojin Isra'ila da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna sun zafafa hare-hare a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suke mamaye suna cin zalin Falasdinawa da wurarensu masu tsarki, da dukiyoyi, ciki har da Gabashin Birnin Kudus, inda suka kashe Falasdinawa akalla 1,006 tare da jikkata sama da 7,000.

Isra'ila ta mamaye Gabashin Kudus a lokacin yakin Larabawa da Isra'ila a 1967. Ta mamaye birnin a shekarar 1980 a wani mataki da kasashen duniya ba su amince da shi ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#