Sport
Dollar
40,4071
0.01 %Euro
47,1614
0.49 %Gram Gold
4.351,0500
0.01 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Netanyahu wanda a kwanakin baya aka yi wa tiyatar mafitsara sannan kuma aka saka masa na'ura a zuciyarsa domin taimaka wa bugun zuciyarsa, likitoci a halin yanzu sun gano yana fama da kumburin hanji.
Likitoci sun gano Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, na fama da kumburin hanji wanda hakan zai sa ya huta na tsawon kwanaki uku, kamar yadda ofishinsa ya sanar a ranar Lahadi.
Netanyahu, wanda yake da shekara 75, ya kamu da rashin lafiya cikin dare, inda aka gano yana fama da kumburin hanji da rashin ruwa a jikinsa. A halin yanzu, yana karɓar magani ta hanyar yi masa ƙarin ruwa, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.
Ofishinsa ya bayyana cewa yana samun lafiya kuma, "A karkashin jagorancin likitocinsa, firaminista zai huta a gida na tsawon kwanaki uku kuma zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati daga can."
An saka wa Netanyahu na’urar taimaka wa bugun zuciya a shekarar 2023, sannan a watan Disamba na bara, ya yi fama da ciwon mafitsara inda aka yi masa tiyata.
A cewar tashar Channel 12, firaministan ba zai halarci zaman majalisar Knesset na ranar Lahadi ba, kuma zaman shari'arsa a gaban Kotun Gundumar Tel Aviv an shirya shi a ranar Litinin.
Comments
No comments Yet
Comment