Dollar

40,6001

0 %

Euro

46,5738

0.42 %

Gram Gold

4.291,3200

0.41 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Sanarwar ta yi kira ga "dukkan kamfanoni su dakatar da kowane irin nau'in hulɗa da tasoshin jiragen ruwan Isra'ila.

Houthi ta sake ƙaddamar da shirin 'hana jiragen sojin ruwa' wucewa zuwa Israʼila

Kungiyar Houthi ta Yemen ta sanar a ranar Lahadi cewa ta yanke shawarar “ƙara ƙaimi” a ayyukan sojojinta tare da fara aiwatar da mataki na hudu na “hana jiragen sojin ruwa wucewa” Isra’ila, a matsayin martani ga kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza.

A cikin wata sanarwa da sojojin kungiyar suka fitar, Houthi ta bayyana cewa wannan matakin ya haɗa da “nuna wa dukkan jiragen ruwa mallakar kowane kamfani da ke hulɗa da tasoshin jiragen ruwa na Isra’ila, ba tare da la’akari da ƙasar da kamfanin ya fito ba ko wurin da sojojinmu za su iya kaiwa ba.”

Sun kuma yi gargadi cewa jiragen ruwa na iya zama abin hari ba tare da la’akari da inda suke nufa ba, a duk inda makamanmu ko jiragenmu masu saukar ungulu za su iya kaiwa.

Kungiyar ta kuma yi kira ga “dukkan ƙasashe, idan suna son kauce wa wannan lamari, su matsa wa abokan gaba lamba don su dakatar da hare-harensu da kuma cire takunkumin da aka sanya wa Gaza. Babu wani mutum mai ‘yanci a wannan duniya da zai amince da abin da ke faruwa.”

Tun bayan da sojojin Isra’ila suka ci gaba da kai hare-hare kan Gaza a watan Maris, bayan watanni biyu na tsagaita wuta mai rauni, Houthi sun ƙara yawan kai harin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa kan Isra’ila.

Tun daga watan Nuwamba 2023, kungiyar ta kuma kai hare-hare kan jiragen kasuwanci a cikin Tekun Bahar Maliya da Gabar Tekun Aden, da Tekun Larabawa don nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza, inda sama da mutum 59,800 suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren Isra’ila.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#