Sport
Dollar
40,6043
0.01 %Euro
46,5648
0.41 %Gram Gold
4.293,1700
0.45 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce dole a bai wa MDD damar ba da ko wane nau’in agaji mai yawa ga iyalai da ke tsananin buƙata a Gaza.
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargaɗi game da yadda matsalar yunwa ke daɗa ƙamari a Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda ya bayyana shi a matsayin "bala’in da bil’adama ya haddasa" yayin da ƙawanyar da Isra’ila ke ci gaba da yi wa yankin ta jefa musamman yara cikin uƙubar yunwa.
"Yunwa na ƙara ƙamari a Gaza kuma mutane suna mutuwa," kamar yadda asusun ya bayyana a shafinsa na X ranar Litinin, inda ya bayyana irin matsanancin halin da ake rayuwa a ciki a ƙarƙashin ƙawanyar Isra’ila.
Yayin da yake bayyana cewa "yunwa mai iya kisa a cikin yara ta kai wani mataki na bala’i," UNICEF ya ce "samun abinci na da matuƙar wuya kuma ruwa mai tsafta ya ragu bisa yadda ake so ya kasance a matakan ko-ta-kwana."
"An yi mugun rage ba da agaji kuma akwai haɗari sosai wajen samunsa," in ji asusun na MDD.
Yayin da yake jaddada buƙatar gaggawar [kai ɗauki] na yanayin, asusun UNICEF ya ce: "Ya isa haka. Dole a bai wa MDD damar isar da agaji mai yawa ga iyalai a duk inda suke."
"Azabtarwa da yunwa wani abin tsoro ne ga yara da iyalai a Gaza," in ji asusun, yana mai jaddada cewa dole a ba da damar shigar da kayan agajin gaggawa wurin da aka yi wa ƙawanya.
Yunwa a yanayin kisan kiyashi
Gargaɗin asusun yara na UNICEF na zuwa ne lokacin da Isra’ila take ci gaba da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a yankin da aka yi wa ƙawanya, lamarin da bai nuna wata alamar tsayawa ba, duk da cewa matsananciyar tamowa na kashe mutane.
Aƙalla mutum 18 ne suka mutu sakamakon matsananciyar yunwa cikin sa’o’i 24 da suka gabata, lamarin da ke nuna yadda masifar ke daɗa ƙamari yayin da hare-haren bam babu ƙaƙƙautawa da kuma hana mutane [agaji] ke tura mutane cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Isra’ila ta kashe sama da Falasɗinawa 59,000, yawancinsu mata ne da ƙanan yara, a kisan kiyashin da ƙawanyar da take yi a birnin.
Kimanin Falasɗinawa 11,000 ne ake fargabar cewa ɓaraguzan gine-gine da aka lalata sun binne su, in ji kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA .
Sai dai kuma matasa, suna ganin adadin waɗanda aka kashe ya fi adadin da hukumin Gaza suka fitar, inda suka yi kiyasin cewa zai iya kai kimanin mutum 200,000.
A tsawon lokacin kisan kiyashin, Isra’ila ta lalata yawancin gine –ginen garin kuma ta raba mutanesa da gidajensu.
Ta kuma hana shigar da agajin gaggawa da ake buƙata, inda ta bai wa wata ƙungiyar ba da agaji mai cike da ce-ce-ku-ce da Amurka ke goyon baya kaɗai damar shiga. Ƙungiyar an samar da ita ne domin kauce wa aikin agajin MDD.
Comments
No comments Yet
Comment