Sport
Dollar
40,2990
0.1 %Euro
46,9561
-0.45 %Gram Gold
4.323,8300
0.11 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A yayin da ake ci gaba da alhinin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, TRT Afrika ta yi nazari kan wasu daga cikin kalaman shugaban da suka yaɗu kamar wutar daji, har ma wasu suka zama sara.
Da zarar an ce mutum ya mutu, to mutane kan yi ta tunawa da abubuwa da yawa da ya gudanar a rayuwarsa, musamman ayyukansa na alkairi da kuma wasu kalaman da ya taba furtawa.
A yayin da ake ci gaba da alhinin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, TRT Afrika ta yi nazari kan wasu daga cikin kalaman shugaban da suka yaɗu kamar wutar daji, har ma wasu suka zama sara.
“Ni na kowa ne, babu wanda ya mallake ni” – (2015)
Tun a ranar da aka rantsar da shugaba Buhari a wa’adin mulkinsa na farko, wato ranar 29 ga Mayun 2015, sabon shugaban ya bayyana sadaukarwarsa ga ‘yan kasa baki-daya.
Shugaba Buhari ya ce, “Bayan rantsuwar da na yi da Littafi Mai Tsarki 'yan mintuna kaɗan da suka gabata, na dauki aniyar riƙe alƙawarin rantsuwar da kuma zama Shugaban Ƙasa ga dukkan 'yan Nijeriya.
“Ni na kowa ne kuma babu wanda ya mallake ni. Wasu mutane ƙalilan sun bayyana fargabar cewa idan na koma kan mulki zan hukunta su. Wannan fargaba ba ta da tushe. Ba zan tuna baya ba. Abin da ya faru ya riga ya wuce.”
Wannan jawabi ya ja hankalin ‘yan kasar matuka, musamman masu fargabar cewa zai nuna wariya ga wasu mutane ko wani bangaren kasar, tare da fifita wasu daban.
“Hurumin matata shi ne kicin, falo, da turakata” – (2016)
Yayin wata ziyara da ya kai kasar Jamus, Shugaba Buhari ya yi jawabi ga manema labarai tare da shugabar gwamnatin Jamus a wancan lokacin, Angela Merkel, inda aka tambaye shi game da wasu kalaman da matarsa ta yi.
Tun da fari, an ambato maidakin nasa, Aisha Buhari tana nuna tantama kan ko za ta goyi bayan mijinta a takarar neman wa’adi na biyu, bayan da ta ce ta lura cewa “wasu tsirarun mutane sun kankane gwamnatinsa”.
Da yake martani kan maidakin nasa, Buhari ya fada ranar 16 ga Oktoban 2016 cewa, “Ban san wace jam’iyya matata take ba, amma na san huruminta ya tsaya ne a kicin, falo, da turakata”.
Daga nan ne sai mutane suka dauki sarar cewa aikin mata ya tattara ne kan hidimtawa mazajensu ta hanyar girke-girke da kuma biyan bukatun zamantakewar aure.
An yi ta jin matasa na zolayar abokai da kawayensu da kalamai kamar, “’yan dakin girki”, “‘yan turaka”, ko abin da masu Engausa ke cewa “oza rum”.
“Malalatan matasa” – (2018)
Ranar 18 ga Afrilun 2018, a wajen wani taro na kasuwanci da Kungiyar Hadin-kan Kasashe Rainon Birtaniya, Commonwealth ta shirya a birnin London, shugaba Buhari ya yi wani tsokaci kan matasan Nijeriya.
Shugaban ya ce, “Muna da matasa da yawa. Fiye da kashi 60 na al’ummar ‘yan kasa da shekara 30 ne. Da yawansu ba su je makaranta ba kuma suna ikirarin cewa Nijeriya ƙasa ce mai arzikin mai, don haka za su shantake su ƙi yin komai su kuma sa ran gwamnati ta ba su gidaje da kiwon lafiya da ilimi kyauta.”
Kalaman da shugaba Buhari ya yi na cewa yawancin matasan kasarsa malalata ne, abu ne da mutane da dama ke ganin dacewarsa ba, musamman a bainar kasashen duniya kuma a taron kyautata alakar tattalin arziki.
Da alama kalaman sun fusata wasu matasa, inda suka shiga shafukan sada-zumunta suna zunde da wallafa sakonni da maudu’in #LazyNigerianYouths, wato #MalalatanMatasanNijeriya.
“Ban mutu ba, ni din ne” – (2018)
A karshen shekarar 2018, an yi ta yada jita-jitar cewa shugaba Buhari ya rasu, kuma mutumin da ake gani a zahiri wai musayarsa ne. Wannan ya zo ne sakamakon zargin wasu ‘yan adawar gwamnatin kasar.
A lokacin shugaba Buhari mai shekara 75 yana fama da rashin lafiyar da ta kai shi jinya a kasashen waje tsawon watanni. Kuma a watan Fabrairun shekarar da ke tafe, 2019 ake sa ran zai nemi wa’adin mulki na biyu.
Buhari ya bayyana cewa “Wasu mutane suna tunanin an musanya ni da wani, amma ni din ne, ina tabbatar muku da wannan".
Ya kara da cewa, “Mutane da yawa sun yi fatan a ce na mutu a lokacin da ba ni da lafiya. Wasu ma har tuntuɓar mataimakin Shugaban Ƙasa suka yi don suna fatan su zama mataimakinsa, saboda sun ɗauka na mutu.”
“’Yan sharholiya” – (2022)
A wata hira da wani gidan talabijin mai zaman kansa a Nijeriya mai suna Tambari TV da aka wallafa ranar 2 ga Nuwamban 2022, mai tambaya ya nemin jin ta-bakin shugaba Buhari kan batun sahihanci zabuka a kasar.
A wancan lokacin, Buhari ya ba da misali da wasu zabukan gwamnoni da aka yi a jihohin Anambra da Ekiti da Osun, wadanda jam’iyyun hamayya suka lashe, yana mai kafa hujjar rashin tsoma bakin gwamnatinsa kan adalcin zabukan.
Daga nan sai ya ce, "Zan tunawa ‘yan Najeriya da yake su sharholiya ta yi musu yawa. Abin da kawai suka ga dama suke magana a kai, ba a tsayawa a yi zurfin tunani…"
Wadannan kalamai sun ja hankali sosai, kasancewa abin da kafafen labarai musamman na sada-sumunta suka yi ta maimaitawa shi ne, Buhari ya kira ‘yan Nijeriya da “’yan sharholiya”.
Comments
No comments Yet
Comment