Dollar

40,2342

0.14 %

Euro

46,9313

-0.33 %

Gram Gold

4.328,6200

-0.15 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Saƙonnin ta'aziyyar wasu manyan Nijeriya kan rasuwar Muhammadu Buhari

A yayin da ake ci gaba da alhinin rashin tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, jiga-jigan siyasar kasar da tsofaffin shugabanni na fitar da saƙonnin alhini da ta’aziyya:

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu:

A saƙon da ya fitar a ranar Lahadin nan da Buharin ya rasu, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana mutumin da gada a matsayin cikakken ɗan kishin ƙasa, soja kuma dattijo.

Tinubu ya ƙara da cewa Buhari mutum ne da ya sadaukar da kansa, wanda ayyukansa za su ci gaba da kasancewa har bayan rayuwarsa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar:

Shi ma tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya ce rasuwar Buhari babbar asara ce ba kawai ga iyalansa ko mutanen Daura ba, har ma ga ƙasa baki daya.

Atiku ya kuma bayyana Buhari a matsayin shaidar juriyar Nijeriya.

“Tun daga fagen daga har zuwa shugabanci, ya yi aiki tare da nuna shi soja ne mai ɗabi’u masu daraja kuma shugaba da ke da aniyar kawo sauyi.”

Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan:

A nasa saƙon alhini da ta’aziyya, tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ce Nijeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun shugabanninta kuma “ni na yi rashin abokin aiki da nake girmamawa.”

Jonathan ya ce Buhari shugaba ne da ake ƙauna a dukkan matakan al’umma saboda tsarkakakkiyar zuciya da dattijantakarsa da kuma yin rayuwa abar koyi.

“Za a ci gaba da tuna da shi a matsayin shugaba jajirtacce, jami’in soja mai halaye nagari, wanda ya kuma bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da cigaban ƙasarmu.”

Tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo:

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ma ya bayyana alhininsa game da mutuwar tsohon Shugaba Buhari, inda a sakon da ya fitar ya ce Buharin ya rasu a muhimmin lokacin da kasar take bukatar basira da gogewar tsofaffin shugabanni don magance kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu.

Obasanjo ya bayyana Buhari a matsayin ɗan kishin ƙasa, wanda ya taka muhimmiyar rawa a matsayin soja, jami’in gwamnati kuma dattijon ƙasa.

Tsohon Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida:

Tsohon shugaban Nijeriya na mulkin soji Ibrahim Badamasi Banbangida ma ya fitar da nasa sakon ta’aziyyar rasuwar Buhari inda ya ce “Buhari abokina ne, ɗan’uwana kuma mai kishin kasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga Nijeriya.”

Babangida ya ce tun haduwar su da Buhari a makarantar soji a 1962, ya san shi da zama mai riƙo da addini, mai imani, ƙanƙan da kai da dattijantaka.

Tsohon Mataimakin Buhari Yemi Osinbajo:

Shi ma mutumin da ya yi wa Buhari Mataimakin Shugaban Kasa tsawon shekaru takwas Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana alhininsa game da mutuwar tsohon mai gidansa.

Osinbajo ya ce Nijeriya ta yi rashin ɗan kishin kasa na gaske, wanda ya saudakar da rayuwarsa wajen hidimta wa kasar da da yake kauna.

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya:

Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta fitar da nata sakon alhinin da ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban Nijeriyar da ya yi takara a karkashinta har sau biyu kuma ya yi mulki tsawon shekaru takwas.

APC ta ce Nijeriya ta yi rashin babban ɗan kishin kasa, shugaba abin koyi wanda ya yi rayuwa mai cike da tsagwaron sadaukar da kai da dattijantaka.

Babbar Jam’iyyar Adawa ta PDP:

Babbar Jam’iyyar Adawa ta PDP a Nijeriya ma ta fitar da sakon alhini da ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

Sanarwar da jam’iyyar ta fitar ta bayyana Buhari a matsayin jajirataccen shugaban soji da farar hula da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa kasa.

Jam’iyyar ta ce za a ci gaba da tunawa da rawar da Buhari ya taka wajen gina kasa a lokacin da yake gwamnan tsohuwar jihar Borno da Ministan Man Fetur da Shugaban PTF da Shugaban Ƙasa na mulkin soja da na mulkin farar hula zababbe.

Shugabanni na da da na yanzun da manyan jam’iyyun Nijeriya da ke fitar da sakon ta’aziyya da alhinin rasuwar Buhari, sun bayyana samun labrin rasuwar cikin bakin ciki. kuma suna yi masa fatan samun jinƙan Ubangiji.

Tuni dai mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya isa birnin Landan domin tahowa da gawar tsohon shugaban ƙasar.

Ana sa ran gudanar da jana’izar tsohon shugaban a Daura da zarar gawar ta isa Nijeriya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#