Publication : 3 February 2026
Update : 3 February 2026
Tauraron Nijeriya ya ci ƙwallo, ya bayar da assist a wasan da Galatasaray ta doke Kayserispor 4–0
Tauraron ɗanwasan Nijeriya Victor Osimhen ya ci ƙwallo a bugun ɗurme tare da bayar da tallafin ƙwallo a wasan da Galatasaray ta doke Kayserispor da ci 4–0 a gasar Super Lig ta Turkiyya. TRT Hausa
Ƙwallon da Osimhen ya ci ita ce ta 200 a rayuwarsa ta ƙwararren ɗanƙwallo, wani muhimmin mataki da ke nuna irin nasarar da ya samu a harkar kwallon kafa. TRT Hausa
Osimhen ya cim ma wannan matsayi ne ta hanyar buga wa ƙungiyoyi da dama a Turai, inda ya ci ƙwallo 76 a Napoli, 20 a Charleroi, 18 a Lille, da 51 a Galatasaray. TRT Hausa
A fagen ƙwallon ƙasa-da-ƙasa, Osimhen ya ci ƙwallo 35 wa tawagar Super Eagles, inda a yanzu yake matsayi na biyu a yawan ƙwallaye, bayan Rashidi Yekini da ke gaba da shi da ƙwallo biyu. TRT Hausa
A tarihin ƙwallon Nijeriya, ‘yan wasa kaɗan ne suka haura ƙwallo 200, ciki har da Rashidi Yekini, Odion Ighalo da Yakubu Aiyegbeni, lamarin da ke nuna girman nasarar da Osimhen ya samu. TRT Hausa
Kai Osimhen mai shekaru 27 wannan mataki na ƙwallo 200 na nuna ya shiga sahun manyan zakarun ‘yanƙwallon Nijeriya, tare da sauran damar ƙara yawan ƙwallaye a gaba. TRT Hausa
Historic direct elections begin in Somalia’s Galmudug region
Registered voters across 11 districts in Galmudug headed to the polls to elect members of the regional house of representatives and local councils.
US government redraws map of Africa at global AIDS conference
The US State Department said it takes full responsibility for the confusion and misrepresentation after the map mislabeled every African country.
Fastest growing Ebola outbreak ever kills over 1,500 in DR Congo
The outbreak declared on May 15 is unlike most previous Ebola outbreaks because the Bundibugyo virus responsible for it has no approved vaccines or treatments.
Most Read
All rights reserved. Newstimetr © 2023