An cafke su ne bayan wani aikin sirri mai suna “MONITUM”

MIT ta kama mutane biyu da ake zargi da aiki wa Mossad

 

Hukumar leƙen asirin Turkiyya (MIT) ta kama mutane biyu da ake zargi da yin aiki wa hukumar leƙen asirin Isra’ila ta Mossad, bayan wani aikin yaƙi da leƙen asiri mai sarkakiya da aka sanya wa suna “MONITUM.” TRT Hausa

Majiyoyin tsaron Turkiyya sun ce an kama Mehmet Budak Derya da Veysel Kerimoglu ne a wani samame na haɗin gwiwa tsakanin MIT, ofishin Babban Mai Shigar da Ƙara na Istanbul da kuma sashen yaƙi da ta’addanci na rundunar ‘yansandan Istanbul. TRT Hausa

Bincike ya nuna cewa Derya, injiniyan hakar ma’adanai, ya faɗaɗa kasuwancinsa zuwa cinikayyar ƙasa da ƙasa, lamarin da ake zargin ya jawo hankalin leƙen asirin Isra’ila, inda daga bisani aka haɗa shi da jami’an Mossad ta hanyar wani kamfani na bogi. TRT Hausa

Haka kuma ana zargin wani jami’in Mossad ya nemi a ɗauki Veysel Kerimoglu aiki tare da Derya, inda aka umarce su da su riƙa bayar da rahoto kan ayyukansu da hulɗoɗinsu a wasu ƙasashe. TRT Hausa

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#